"Na San Waɗanda Suka Biya Kudi kafin a Naɗa Su Minista," El Rufai Ya Tona Asiri

"Na San Waɗanda Suka Biya Kudi kafin a Naɗa Su Minista," El Rufai Ya Tona Asiri

  • Malam Nasir El-Rufai ya sake ƙaryata zargin cewa ya bar APC ne saboda bai samu muƙami a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba
  • Tsohon gwamnan Kaduna ya ce bai nemi a ba shi muƙami ba amma ya san waɗanda suka biya kuɗi kafin a naɗa su a matsayin minista
  • Wannan kalamai na El-Rufai na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan ya sanar da barin APC tare da komawa jam'iyyar SDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sake jaddada cewa ba rashin naɗa shi minista ne ya kore shi daga jam'iyyar APC ba.

El-Rufai ya bayyana cewa ya bar jam'iyya mai mulki ne sabida ta sauka daga manufofin da suka kafa ta a kansu.

Tinubu da El Rufai.
Tsohon gwamnan Kaduna ya musanta zargin cewa saboda hana shi mukami ya bar APC Hoto: @ElRufai
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan ya yi wannan bayani ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa, wadda aka wallafa yau Alhamis, 13 ga watan Maris, 2025.

Kara karanta wannan

El Rufai ya bayyana yadda suka yi da Buhari kan batun ficewarsa daga APC zuwa SDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya bayyana cewa sai da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya amince masa sannan ya sauya sheka daga APC zuwa SDP.

A cewarsa, Buhari ya faɗa masa cewa shi yanzu ya tsame hannu a harkokin siyasa, ya koma uban ƙasa.

El-Rufai ya bar APC saboda za a kore shi?

Da aka tambaye kan ko ya bar APC ne saboda gudun kada a kore shi, Malam El-Rufai ya ce da ma sun kore shi da ya samu sauƙi wajen yi wa jama'a bayani.

"Ni da sun kore ni ma da ya fi mani sauƙi domin na sha faɗa cewa idan na bar jam'iyyar APC na yi ritaya daga siyasa.
"Saboda haka da sun kore ni, sun samar mani hanyar da zan yi bayanin me ya sa na bar APC. Amma kamar yadda na sha faɗa ni ban bar jam'iyyar APC ba, ita ta bar ni."

Kara karanta wannan

"Da shi muka shirya yaƙar Atiku," Wike ya tona asirin gwamna a Arewacin Najeriya

El-Rufai ya tona asirin naɗin ministoci

Haka nan da aka tambaye shi kan raɗe-raɗin da ke yawo cewa ya bar APC ne saboda hana shi minista, tsohon gwamnan ya ce bai taɓa neman muƙami a wurin Tinubu ba.

"Haka suke cewa amma ni na nema ne? Ni na san waɗanda suka ɓiya kudi kafin a ba su muƙamin minista. Amma ni shugaban ƙasa ya roƙe ni a fili balle ya musa, a Kaduna ya nemi na zo na yi aiki tare da shi.
"Duk da haka ban ce na yarda ba sai da muka zauna da shi, ya gaya mani yana son warware matsalar lantarki da ta hana kasar nan ci gaba, sannan na yarda zamu yi aiki, daga baya kuma ya canza."

- Nasir El-Rufai.

Gwamnatin Tinubu ke rura rikicin jam'iyyu

A wani labarin, kun ji cewa El-Rufai ya yi ikirarin cewa gwamnatin Najeriya ta APC ce take ƙulla duk rigingimun da ke faruwa a jam'iyyun adawa.

El-Rufai ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu ce ta ke ɗaukar nauyin tayar da zaune tsaye a cikin waɗannan jam’iyyun domin cimma burinfa cikin sauƙi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel