Tsohon Gwamna Ya Fice daga Jam’iyyar APC Mai Mulki? An Samu Gaskiyar Bayani

Tsohon Gwamna Ya Fice daga Jam’iyyar APC Mai Mulki? An Samu Gaskiyar Bayani

  • Tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi ya karyata jita-jitar ficewarsa daga APC, yana mai cewa har yanzu yana cikinta
  • Bayan ficewar El-Rufai daga APC zuwa jam'iyyar adawa ta SDP, mutane da dama sun fara hasashen Fayemi zai bi sahu
  • Fayemi ya bayyana cewa yana goyon bayan karfafa dimokuradiyya a cikin jam’iyya da kuma hada kan ‘ya’yanta
  • Tsohon ministan ya ce har yanzu akwai damar APC ta gyara matsalolinta kafin lokaci ya kure mata musamman game da zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ado-Ekiti - Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi, ya musanta jita-jitar cewa ya fice daga jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Jita-jita ta karade kafafen sada zumunta cewa Kayode Fayemi na daga cikin masu shirin barin jam’iyyar APC saboda sabanin cikin gida.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani kan sauya shekar El Rufai, ta fadi shirin da take yi

Tsohon gwamna ya magantu kan jita-jitar ficewa daga APC
Tsohon Gwamna, Kayode Fayemi ya musanta labarin ficewa daga APC. Hoto: @OfficilaAPCNg.
Source: Twitter

Wane martani Fayemi ya yi kan barinsa APC?

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwar da tsohon gwamnan ya wallafa a shafin X a jiya Litinin 10 ga watan Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai a cikin sakon da ya wallafa, Fayemi ya bayyana cewa har yanzu yana tare da jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Sanarwar ta ce"

"Na ci karo da wasu rahotanni cewa na sauya sheka daga APC zuwa wata jam'iyyar, kamar yadda na saba fada a baya, ni dan jam'iyya (APC) ne kuma ba ta sauya zani ba."
"Har yanzu ina ganin ba mu yi latti ba domin kawo sauye-sauye a tsarin yadda ake gudanar da jam'iyyar da kuma mulkin Najeriya domin bunkasar dimukradiyya."
Tsohon gwamna ya yi magana game da sauya sheka daga APC
Kayode Fayemi ya ƙaryata labarin barin APC da ake yadawa. Hoto: Kayode Fayemi.
Source: Facebook

Fayemi ya bukaci kawo gyara a tafiyar APC

Dr. John Kayode Fayemi ya ce ko da yake yana goyon bayan bude kofa da hada kan jam’iyyar, bai fice daga jam’iyyar ba.

Kara karanta wannan

'Mutuwa ce kawai za ta raba ni da APC,' Tarihi ya tuna maganganun El Rufa'i

Fayemi ya bayyana cewa yana fatan jam’iyyar APC za ta duba matsalolinta na cikin gida da nufin gyara kurakurai kafin lokaci ya kure.

Ya jaddada cewa matsayinsa kan jam’iyyar bai canza ba, kuma har yanzu yana cikin wadanda suka kafa APC tun farko.

Amma Fayemi ya nuna cewa yana da ra’ayi daban, yana fatan jam’iyyar za ta tashi tsaye domin hada kan mambobinta.

Ya kara da cewa yana maraba da ci gaban jam’iyyar bisa hanyar gaskiya, shawarwari da fahimtar juna tsakanin shugabanni da mambobi.

Wannan matakin Fayemi ya bayyana irin yadda wasu ‘yan siyasa ke kokarin gyara jam’iyya daga ciki maimakon ficewa gaba daya.

Ya ce tun da farko yana da kima a jam’iyyar kuma bai ga dalilin da zai sa ya fice daga cikinta ba.

Fayemi ya kuma bukaci shugabannin APC su maida hankali wajen dinke baraka da tabbatar da daidaito da adalci a jam’iyyar.

El-Rufai ya fice daga APC zuwa SDP

Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya watsar da jam'iyyar APC, ya koma SDP mai adawa.

Kara karanta wannan

Daga sauya sheka, El Rufa'i ya fadi yadda zai jawo rugujewar APC a Najeriya

El-Rufai ya dauki wannan mataki ne yayin da alaka ta fara tsami tsakaninsa da APC da kuma gwamnatin Bola Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.