'Mutuwa ce Kawai za Ta Raba Ni da APC,' Tarihi Ya Tuna Maganganun El Rufa'i
- Bayan ficewarsa daga APC, tarihi ya tono wasu maganganun El-Rufa'i da kalamansa na cewa ba zai taɓa barin jam’iyyar ba
- A shekaru uku da suka wuce, tsohon gwamnan jihar Kaduna ya bayyana cewa APC tana cikin jerin abubuwan da ya ƙirƙira
- A 2022, El-Rufa'i ya sha alwashin cewa idan ya bar APC, to hakan na nufin ya daina siyasa gaba ɗaya ba wata jam'iyya da zai koma
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Bayan ficewar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i daga jam’iyyar APC, an tuno kalamansa na baya, inda ya taɓa cewa ba zai taɓa barin APC ba har abada.
El-Rufa’i ya bayyana hakan ne a wata hira kai tsaye da aka watsa ta gidajen rediyon Kaduna a 2022, inda ya musanta jita-jitar cewa yana shirin sauya sheƙa daga APC.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta wallafa cewa tsohon gwamnan ya ce yana daga cikin mutum 37 da suka assasa jam’iyyar APC, don haka yana kallon jam’iyyar a matsayin ɗaya daga cikin ’ya’yansa.
2022: El-Rufa’i ya nuna amincewa da APC
A cikin tattaunawar da ya yi a 2022, El-Rufa’i ya ce babu wani dalili da zai sa ya bar APC, yana mai cewa:
“Lokacin da na bar APC, to hakan yana nufin na daina siyasa gaba ɗaya.”
A lokacin, tsohon gwamnan ya musanta rahoton da ke cewa ya cire tutar APC daga motarsa ta ofis, yana mai cewa dokar gwamnatin jiha ce a sauke tutoci bayan ƙarfe 6:00 na yamma.
Ya ce:
“Idan tuta tana a kan sandar gini, ana sauke ta bayan ƙarfe 6:00 na yamma. Idan kuma tana jikin mota, ana rufe ta. Wannan ba sabon abu ba ne.”
El-Rufa'i ya musanta sauya sheƙa a 2022

Kara karanta wannan
"Mai jiran gado": Martanin 'yan Najeriya bayan El Rufai ya fice daga APC zuwa SDP
A lokacin hirar, El-Rufa’i ya karyata ikirarin da ake yi cewa yana shirin sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya saboda matsalar zaɓen mataimakin shugaban ƙasa a APC.
A cewarsa:
“Tun farko sun ce ina son zama shugaban ƙasa, daga baya suka ce ina son zama mataimaki, yanzu kuma sun dawo suna cewa ina son zama daraktan yaƙin neman zaɓe.”
A lokacin, El-Rufa'i ya kara da cewa ya ce irin waɗannan jita-jita ba su da tushe, kuma ana yinsu ne domin ɓata masa suna.

Source: Facebook
Nasir El-Rufa'i ya fita daga APC a 2025
Bayan shekaru uku, El-Rufa’i ya fice daga APC, hakan yasa ake tambaya ko yana nufin ya sauya ra’ayin da ya bayyana a baya cewa ba zai bar jam’iyyar ba.
Baya ga hakan, an jiyo cewa tsohon gwamnan ya koma jam’iyyar SDP, yana mai cewa zai jagoranci ƙawancen jam’iyyun adawa domin fuskantar APC a 2027.
El-Rufa'i ya ziyarci Atiku Abubakar
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ziyarci Wazirin Adamawa watau Atiku Abubakar.
Tsohon gwamnan ya ziyarci Atiku Abubakar ne a gidansa kuma sun yi buda baki tare da wasu manyan 'yan siyasa a fadin kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Ibrahim Yusuf, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

