Ana Raɗe Radin Atiku Ya Bar PDP, Ganduje da Barau Sun Sharewa Tinubu Hanya a Jihohi Arewa 19

Ana Raɗe Radin Atiku Ya Bar PDP, Ganduje da Barau Sun Sharewa Tinubu Hanya a Jihohi Arewa 19

  • Gamayyar kungiyoyin magoya bayan Atiku Abubakar a jihohin Arewa 19 sun fice daga jam'iyyar PDP, sun koma APC mai mulkin Najeriya
  • Shugaban APC, Abdullahi Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau I. Jibrin sun tarbi masu sauya shekar a wani taro a Abuja
  • Masu sauya sheƙar sun sha alwashin marawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu baya domin ya samu nasara a zaɓen 2027 maimakon Atiku

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I Jibrin, sun karɓi ɗaruruwan magoya bayan Atiku Abubakar, daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya.

Magoya bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasar a zaɓen 2023, waɗanda suka yi aiki tare da shi a PDP, sun sanar da komawarsu APC a wani taro da aka shirya a Abuja.

Kara karanta wannan

Barau ya karbi sakataren malaman Kwankwasiyya da 'yan uwan Abba a APC

Ganduje da Barau.
2027: Ganduje da Sanata Barau sun karɓi magoya bayan Atiku da suka dawo APC a Arewa
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce shugabannin gamayyar ƙungiyoyin magoya bsyan Atiku daga shiyyoyin Arewa sun lashi takobin marawa Bola Tinubu baya a zaɓen 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagororin masu sauya shekar su ne Malami Nasidi, Musa Yahaya da Kabiru Gambo, waɗanda su ne shugabaannin ƙungiyoyin a Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas.

Jam'iyyar APC ta yi babban kamu

Da yake jawabi a wajen taron, Sanata Barau Jibrin ya bayyana sauya sheƙar waɗannan magoya baya a matsayin babban kamu ga jam’iyyar APC.

“Wannan babbar nasara ce, jam'iyyarmu ta yi kamu. Shugaban ƙasa mutum ne mai nagarta, yana ƙoƙarin sake farfaɗo da Najeriya. Yana aiki tukuru domin mayar da ƙasar nan kan turba mai kyau.
“A APC, ba mu nuna wariya. Duk wanda ya shigo jam’iyya yau yana da dama daidai da wanda ya shafe shekaru a ciki. Abin da ke bambanta mutane shi ne ƙoƙarinsu da gudummawar da suka bayar.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ɓarna a Arewa maso Yamma, an kashe mutane 12,000

Sanata Barau ya jinjinawa Ganduje bisa jagorancinsa a APC, musamman wajen lashe zaɓukan gwamnonin da aka gudanar bayan babban zaɓen 2023, in ji Vanguard.

Ganduje ya yi maraba da masu sauya sheƙa

A nasa jawabin, Shugaban APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ji daɗin sauya sheƙar magoya bayan Atiku, ya bayyana Sanata Barau a matsayin gwarzo da ya jagoranci wannan sauyin sheƙa.

"Mu na maku maraba da zuwa jam’iyyarmu. A yau, muna karɓarku a hukumance. Amma kamar yadda aka sanar da ni, bayan azumi, duk mambobinku za su taru a Abuja ƙarƙashin jagorancin Sanata Barau.
"A lokacin ne za mu gayyaci shugaban ƙasa da mataimakinsa tare da Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Wakilai, domin karɓar ku gaba ɗaya, tare da tabbatar da mutuwar PDP a Najeriya, ba a Arewa kaɗai ba.
“Muna maraba da ku cikin jam’iyya mai akidar ci gaba. Jam’iyya ce da ke mutunta doka da oda. Jam’iyya ce da ke tafiya da ƙa’idojin dimokuraɗiyya. Jam’iyya ce da ke karɓar kowa ba tare da nuna bambanci ba.

Kara karanta wannan

Seyi Tinubu da Minista sun dira gidan Buhari a Kaduna, an yada bidiyon

- Abdullahi Ganduje.

Wani jigon APC, Zaharaddeen Yusuf ya ce wannan ƙoƙarin da shugaban jam'iyya da auran ƴan tawagarsa ke yi na cikin shirinsu na kama wasu jihohi a 2027.

Da yake zantawa da wakilin Legit Hausa kan wannan ci gaban, Malam Dini ya ce APC ta shirya tsaf domin faɗaɗa karfin ikonta a babban zaɓe na gaba.

"Ba zan faɗa ba yanzu amma za ku yi mamakin mutanen da za su shigo APC daga nan zuwa 2027, kawai dai ina tabbatar maku wannan na cikin yunƙurinmu na kama wasu jihohi," in ji shi.

Jigon PDP ya yi magana kan zaɓen 2027

A wani labarin, kun ji cewa Bode George ya bayyana cewa Peter Obi ba zai iya kayar da Bola Tinubu ba tare da goyon bayan jam'iyyar PDP ba.

George ya bayyana cewa jam'iyyarsu ta PDP ce kaɗai ke da ƙarfi da goyon bayan da za ta iya kayar da APC a zaɓen 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262