Ramadan: Ɗan Shugaba Bola Tinubu Ya Yamutsa Siyasar Kano a Wurin Buda Bakin Azumi

Ramadan: Ɗan Shugaba Bola Tinubu Ya Yamutsa Siyasar Kano a Wurin Buda Bakin Azumi

  • Seyi Tinubu, ɗan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya girgiza siyasar Kano da ya tara ƙusoshin APC da NNPP suka yi buɗa baki
  • Ɗan shugaban ƙasar ya yi buɗe baki da jiga-jigan ƴan siyasar ne yau Litinin a masallacin Al-Furqan da ke kwaryar birnin Kano
  • Kafin wannan liyafar buɗa baki, ɗan shugaban kasar ya ziyarci fitaccen ɗan kasuwar nan, Aminu Ɗantata a gidansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Ɗan Shugaban Najeriya, Seyi Tinubu, ya yi buda-baki tare da al’ummar Musulmi a birnin Kano a ranar Litinin, 3 ga watan Maris, 2025.

Sheyi Tinubu ya kaddamar da shirin ciyar da marasa galihu da nakasassu a watan Ramadan, wani bangare na shirin tallafa wa matasa watau RHYE.

Buda baki.
Dan shugaban kasa ya yi buɗa baki da ƴan siyasar Kano Hoto: @DeeOneAyekoto
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa taron buda-bakin ya gudana ne a Masallacin Al-Furqan da ke cikin birnin Kano.

Kara karanta wannan

Seyi Tinubu da Minista sun dira gidan Buhari a Kaduna, an yada bidiyon

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan malamai, ‘yan siyasa, da al’ummar gari sun halarci wurin liyafar cin abinci watau buɗe baki da Seyi Tinubu.

Wannan shiri na ciyarwa na daga cikin kokarin gwamnatin tarayya na rage radadin matsin rayuwa da ke addabar al’umma, musamman a wannan wata mai alfarma na Ramadan.

Ɗan Tinubu ya ziyarci Aminu Ɗantata

Kafin taron buda-bakin, Seyi Tinubu ya kai ziyara gidan shahararren ɗan kasuwa, Alhaji Aminu Dantata, da nufin girmama shi da kuma neman shawarwari daga tsofaffin jiga-jigan Arewa.

Alhaji Dantata, wanda fitaccen ɗan kasuwa ne da ke da tasiri a harkokin siyasa da tattalin arziki, ya yaba da shirin ciyarwa da kuma jajircewar Seyi Tinubu wajen tallafa wa al’umma.

Bayan haka, Seyi Tinubu ya ziyarci gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, inda suka tattauna batutuwa da suka shafi ci gaban matasa da rage fatara a jihar.

Yadda ɗan Tinubu ya haɗa ƴan APC, NNPP

Taron buda-bakin ya samu halartar manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban ba kawai daga jam’iyyar APC ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Abuja, sun hallaka tsohon shugaban hukumar tsaro

Bayan kusoshin APC da suka halarci taron, manyan jiga-jigan NNPP sun je wurin daga ciki har da shugaban NNPP na Kano, Hashimu Dangurawa.

Wannan ya nuna cewa, duk da bambance-bambancen siyasa, ana iya hadin gwiwa wajen yin ayyukan alheri da ci gaban al’umma.

Wurin liyafa.
Sheyi Tinubu ya haɗa yan APC da NNPP wuri 1 a jihar Kano Hoto: @Deeoneayekoto
Asali: Twitter

Shirin RHYE zai tallafa matasa

Seyi Tinubu ya bayyana cewa, shirin RHYE zai ci gaba da tallafa wa marasa galihu da matasa a jihohin Najeriya daban-daban.

A cewarsa, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta ci gaba da daukar matakai na rage radadin matsin tattalin arzikin da ƴan Najeriya ke ciki.

Jama’a da dama sun yaba da wannan shiri, suna mai cewa hakan zai taimaka wajen rage yunwa, musamman ga talakawa da nakasassu a wannan wata mai daraja.

Hadin Kai a Siyasa: Sabon Salo a Kano

Taron buɗa-bakin da Seyi Tinubu ya jagoranta a Kano ya janyo hankalin masu fashin baki kan siyasa, musamman ganin yadda ya haɗa manyan jiga-jigan jam’iyyun APC da NNPP a wuri guda.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya amince da kafa sababbin Jami'o'i 11 a Najeriya, an jero sunayensu

A da, ana ganin siyasar Kano a matsayin mai tsananin rikici da bambance-bambancen ra’ayi, amma wannan liyafa ta nuna cewa ana iya samun hadin kai domin ci gaban al’umma.

Masana harkokin siyasa sun bayyana cewa irin wannan haɗin gwiwa na iya zama sabon salo a siyasar Kano, inda ‘yan adawa za su iya yin aiki tare a lokutan bukatar ci gaban al’umma.

Hakan na nuni da cewa, duk da bambancin siyasa, akwai buƙatar hada hannu wajen ayyukan jin ƙai da tallafawa mabukata.

Wani abu da ya fi daukar hankali a wannan taro shi ne yadda Seyi Tinubu ya yi amfani da damar wajen karfafa shirin RHYE, wanda ke da nufin tallafa wa matasa da marasa galihu.

Wannan na iya zama wata hanya ta samun amincewar jama’a, musamman ma a Arewacin Najeriya da ke fama da matsalar fatara da rashin aikin yi.

Gwamnatin Abba ta karya farashin abinci

Kara karanta wannan

Ana ciyar da mabukata a Kano, mutane 91,000 za su samu buda-bakin Ramadan

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Abba Kabir tare da haɗin guiwar manyan ƴan kasuwa sun rage farashin kayan masarufi a jihar Kano.

Hakan ya taimaka wajen rage farashin kayan abinci kamar shinkafa, sukari, fulawa da mai da mutane suka fi amfani da su yau da kullum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262