'Dabarun 2027 ne': An 'Gano' Makarkashiyar APC kan Batun Kirkirar Sababbin Jihohi
- Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam (CHRICED) ta zargi jam'iyyar APC da amfani da shirin kirkirar sabbin jihohi don yaudarar 'yan Najeriya kafin zaben 2027
- Shugaban CHRICED, Ibrahim Zikirullahi, ya ce APC na amfani da shirin a matsayin tarko don samun goyon baya duk da sanin rashin yiwuwar hakan
- Zikirullahi ya gargadi cewa kirkirar sabbin jihohi zai kara tsananta matsalar tattalin arziki, inda yawancin jihohi ke fama da rashin biyan albashin ma’aikata
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Cibiyar Kare Hakkin Dan Adam da Ilimin Zamantakewa (CHRICED) ta caccaki jam'iyyar APC kan batun ƙirƙirar sababbin jihohi.
Kungiyar ta zargi APC da amfani da shirin kirkirar sababbin jihohi 31 don yaudarar 'yan Najeriya gabanin zaben 2027.

Asali: Twitter
Sababbin jihohi: Yadda aka zargi APC da yaudara
Kungiyar ta bayyana shirin a matsayin wata dabara ta karkatar da hankalin jama'a daga matsalolin tattalin arziki da tsaro, cewar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban CHRICED, Ibrahim Zikirullahi, ya bayyana cewa APC na amfani da shirin kirkirar jihohi a matsayin tarko don samun goyon bayan jama'a kafin 2027.
Zikirullahi ya ce wannan shirin wata dabara ce kawai ta siyasa don yaudarar al'umma ba tare da wani niyya na gaskiya ba.
Ya gargadi cewa kirkirar sababbin jihohi zai kara tsananta matsalar kudi, tun da yawancin jihohi ba su iya biyan albashin ma’aikata ba tare da tallafin tarayya ba.
“Wannan shirin ya nuna rashin daukar matsalolin da talakawa ke fuskanta da muhimmanci, illa kawai neman cimma manufofin siyasa."
- Cewar Zikirullahi
An 'gano' makarkashiyar APC a zaben 2027
Zikirullahi ya zargi APC da amfani da shirin don jan hankalin ‘yan adawa su sauya sheka, suna tunanin hakan zai taimaka musu a zaben 2027.
Ya soki 'yan majalisar da suka fi mayar da hankali kan kirkirar jihohi maimakon magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro a kasar.
Daga bisani, Zikirullahi ya ce kamata ya yi a rage yawan jihohin da ba su samun kudin shiga, a kuma mika wasu iko ga gwamnatocin yankuna.
Tsare-tsaren da ake bi domin samar da jiha
Mun kawo muku labarin cewa akwai tsare-tsaren siyasa da kuma na shari'a da ake bi kafin ƙirƙirar sabuwar jiha a Najeriya.
Hakan ya biyo bayan gabatar da bukatu a majalisar wakilai kan kirkirar sababbin jihohi wanda ya jawo ka-ce-na-ce a kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng