Arewa: El Rufa'i Ya Aika Gargadi ga APC da Tinubu kan Zaben 2027
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El Rufa'i ya yada ra'ayin wani dan APC, Uche Diala a kan makomar jam'iyyarsu a kakar zabe mai zuwa
- An bayyana cewa akwai babbar barazanar Bola Ahmed Tinubu ya samu matsala a zaben 2027, kamar yadda Goodluck Jonathan ya samu a baya
- Diala na ganin barazanar rashin nasarar ba za ta rasa nasaba da daga wa hadi da raini da wasu makusantan Tinubu ke nuna wa Arewacin Najeriya ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yada gargadin da aka yi wa jam'iyyarsa na cewa akwai yiwuwar Shugaban kasa, Bola Tinubu ba zai koma kujerarsa ba.
Gargadin na kunshe ne a cikin sakon da wani dan APC, Uche Diala ya fitar, wanda ya nuna yadda jam'iyyar ta hau turbar da tsohuwar gwamnatin PDP, Goodluck Jonathan ta bi har ta fadi zabe.

Asali: Facebook
Wannan na kunshe a sakon da tsohon gwamnan ya wallafa a shafinsa na X mai taken, “2027: Magoya bayan Tinubu a Arewa maso Yamma na wasa da wuta.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sakon, an bayyana yadda 'yan siyasar da ke da kusanci da Bola Ahmed Tinubu ke izgili ga Arewacin Najeriya, duk da neman kuri'a da ake yi daga yankin a kakar zaben 2027.
An gargadi jam'iyyar APC kan zaben 2027
Nasir El Rufa'i ya wallafa sakon da Uche Diala ya fitar, wanda ya bayyana cewa yanzu ba lokaci ne na maganar babban zaben 2027 ba.
Sakon ya ce:
“A zahiri, ya yi sauri a fara maganar zaben 2027 alhali ba a kammala shekaru biyu na wa’adin farko ba, amma abubuwan da ke faruwa a fagen siyasa sun tilasta min yin magana.
Ana son APC ta yi nasara a zaben gaba
Marubucin ya nuna cewa a matsayinsa na halastaccen dan jam’iyyar APC, yana fatan jam’iyyarsa ta yi nasara a babban zabe mai zuwa.
Sokon da ya wallafa ya bayyana cewa:
“A matsayina na dan APC, lallai ina so jam’iyyata ta yi nasara a zaben 2027. Amma a matsayina na mai hangen nesa, ina da damuwa.”
Ya kara da cewa akwai bukayar a dauki darasi daga zaben fidda gwani na APC a shekarar 2019, inda ya rubuta cewa idan ba a yi taka-tsantsan ba, jam’iyyar na iya fadawa irin matsalar da ta sa PDP ta rasa mulki bayan shekaru 16.
Ya kara da cewa:
“Cikin kasa da shekaru biyu kacal na wa’adin mulkin nan, mun shaida yadda dangantaka tsakanin Arewa da shugaba Tinubu, ko kuma gwamnatinsa, ke tabarbarewa da sauri.
"Abin takaici, hakan na faruwa ne sakamakon kalamai da dabi’un da ke fitowa daga yankin Shugaban kasa da kuma mutanen da ke kusa da shi. Wannan shi ne gaskiya.”
An zargi wasu 'yan APC da hargagi
A rubutun Uche Diala, wanda ake ganin El-Rufa'i akwai alamun Nasir El Rufa'i na da irin ra'ayin, an caccaki yadda wasu da aka kira ‘yan siyasar hargagi ke nuna girman kai da isa ga Arewacin kasar nan.

Kara karanta wannan
'Komai ya wuce': El Rufai ya fadi manyan dalilai 3 na tallata Tinubu a zaben 2023
Wannan na iya zama martani ga Abdullahi Ganduje, wanda ya shaida wa 'yan siyasa a Arewa cewa Bola Tinubu zai kammala wa'adi biyu a mulkin kasar nan.
Sakon ya ce:
“Ina so in tunatar da wasu cewa, ba wai rashin kwarewa ko gazawar mulkin Shugaba Goodluck Jonathan ba ne kadai ya sa ya fadi zabe, a’a, amma halayensa da na mutanen da ke kusa da shi dangane da Arewa ne suka jawo masa faduwa, tare da jefa PDP cikin halin da ya sa ta rasa mulki bayan da ta yi ikirarin mulkar Najeriya har tsawon shekaru 60.”
El-Rufa'i: Na san da zargin barazanar gwamnatin APC
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya ce ya na sane da jita-jitar da ke yawo cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin cafke shi.
El-Rufa'i ya ce tun a watan Yuli 2024, lokacin da rahoton Majalisar Jihar Kaduna ya fara yawo, ake ta yayata cewa gwamnati za ta sa a damke shi, amma hakan ba zai firgita shi ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng