Gwamnan Bauchi Ya Shiga Tsaka Mai Wuya, Ana So Ya Fice daga PDP kan Sukar Wike
- Matasan PDP sun gargadi Gwamna Bala Mohammed da ya daina bata sunan jam’iyyar PDP ko kuma ya fice gaba daya daga jam’iyyar
- Kungiyar PDP-YFN ta ce gwamnan na Bauchi yana daukar kansa a matsayin kakakin Arewa alhalin an gargade sa a kan yin hakan
- Matasan sun bukaci Gwamna Bala ya koyi siyasa daga Nyesom Wike yayin da suka nemi ya guji yin abubuwan da za su tozarta PDP
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wata kungiyar matasan PDP ta gargadi gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, da ya daina abinda ke bata sunan jam’iyyar ko kuma ya fice daga PDP.
Matasa sun yi kakkausan suka ga Bala Mohammed saboda zargin cin mutuncin ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike.

Asali: Twitter
Matasan PDP sun taso gwamnan Bauchi a gaba

Kara karanta wannan
Dogara ya tona asirin 2019: "Yadda Wike ya taimaki Bala ya zama gwamnan Bauchi a PDP"
Shugaban kungiyar PDP-YFN, Kwamared Isah Ibrahim, ya bayyana gwamnan a matsayin wanda ke amfani da PDP don cimma burinsa kawai, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamared Isah ya ce gwamnan Bauchi ya zabi sukar manufofin gwamnati ba gaira ba dalili, wanda hakan ke rage darajar PDP a idon 'yan Najeriya.
“Ya kamata Bala Mohammed ya daina tozarta jam’iyyar PDP kamar yadda yake yi a halin yanzu ko kuma ya fice daga jam’iyyar domin ba mambobi da shugabanninta damar gyara ta.
"Ci gaba da cin zarafin PDP ta hanyar sukar manufofin gwamnati da bai fahimta ba, kamar yadda lamarin ya faru kan gyaran haraji, na rage kimar jam'iyyar a idanun 'yan Najeriya."
- A cewar sanarwar Kwamared Isah.
Matasa sun gargadi gwamna kan sukar gwamnati
Kungiyar matasan ta ce gwamnan na Bauchi yana ci gaba da nuna adawa ga kudurorin gyaran haraji duk da amincewar kungiyar gwamnoni kan wannan batu.
Hakazalika, matasan sun zargi Gwamna Bala da daukar kansa a matsayin mai magana da yawun 'yan Arewa duk da an gaya masa ya daina daukar wannan matsayin.
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
“Abin takaici ne yadda har yanzu Bala Mohammed ya kasa gane cewa a yanzu shi kadai ne ke kidansa kuma yana rawarsa a adawar da yake yi kan sake fasalin haraji.
"Ko da a ce Wike bai yiwa Bala martani ba, ya kamata shi gwamnan ya daina adawa da kudurorin gyara haraji tun da har kungiyar gwamnoni ta cimma matsaya a kai."
Kungiya ta gano dalilin 'babatun' gwamnan Bauchi
Kungiyar ta zargi gwamnan na Bauchi da zakalkalewa saboda burinsa na zama dan takarar shugaban kasa na PDP a 2027, "wanda hakan ke haifar da rashin jituwa da Wike".
"Yanzu mun fahimci dalilin Bala Mohammed na kin karbar gyara shi ne yana kallon kasa ne a matsayin wanda zai lashe tikitin takarar shugaban kasa na PDP a 2026 don shiga zaben 2027."
- Inji Kwamared Isah.
Matasan sun bayyana Gwamna Bala a matsayin wanda yake zubar wa PDP mutunci kuma yake bata sunanta saboda halayensa na rashin fahimta.
Kwamared Isah ya ce:
"Wannan babatun da yake yi na kare wani mukami da ya san ba zai samu ba ya sa Bala Mohammed ya zama abin dariya da ke zubar da martabar PDP a idon jam’iyya."
An nemi gwamnan Bauchi ya fice daga PDP
Matasan sun ba Gwamna Bala shawarar yin biyayya ga Wike domin ya koyi yadda ake gudanar da ayyuka masu amfani ga al’umma.
Matasan sun ce babu wani abin a zo a gani da Gwamna Bala ya cimmawa a matsayin sanata, minista, da gwamna, domin bai kai kamo kafar nasarorin Wike a matsayin minista ba.
Kungiyar ta bukaci Wike da ya watsar da maganganun gwamnan Bauchi kuma ya ci gaba da kare mutuncin PDP daga masu amfani da ita don muradunsu.
Matasan sun bukaci Gwamna Bala ya fice daga PDP idan ba zai gyara halinsa ba, don ba da damar inganta jam’iyyar.
Fada ta barke tsakanin Wike da Bala
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an fara musayar bakaken kalamai tsakanin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da ministan Abuja, Nyesom Wike.
Yayin da gwamnan Bauchi ya zargi Wike a matsayin dan siyasar da ya ci amanar PDP ta hanyar goyon bayan Tinubu, shi ma Wike ya ce Bala ya ci amanar Isah Yuguda da Muhammadu Buhari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng