Sakataren Kamfen Gwamna Ya Fice daga APC, Ya Kwance Wa Tinubu Zani a Kasuwa
- Ɗaya daga cikin ƴan APC na farko-farko a jihar Gombe kuma tsohon sakataren kamfen gwamna Inuwa Yahaya ya fice daga jam'iyyar
- Kwamared Adamu Modibbo ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin APC mai mulki ne saboda yadda ta lalata ƙasa maimakon gyara
- Ya kuma caccaki shugaba Bola Ahned Tinubu bisa jefa yan Najeriya cikin kunci da wahalhalu sakamakon manufofinsa na tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Gombe - Ɗaya daga cikin mambobin farko na jam’iyyar APC mai mulki a jihar Gombe, Adamu Modibbo, ya fice daga jam'iyyar.
Adamu Midibbo, tsohon sakataren kwamitin yakin neman zaben gwamna Inuwa Yahaya, ya ce ba zai ci gaba da zama a APC ba saboda halin da ta jefa ƙasa.

Asali: Facebook
Babban jigon siyasar ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da manema labarai a gidansa ranar Litinin da ta gabata, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon sakataren kanfen gwamna ya bar APC
Ya nuna damuwa da takaici kan halin ƙuncin da ƴan Najeriya suka shiga sakamakon tuƙin ganganci na gwamnatin APC a matakin ƙasa.
A cewarsa, tun farko, “APC ta zo da nufin ceto Najeriya daga matsalolin da take fuskanta,” amma ya koka cewa maimakon hakan, ta jefa kasar cikin rudani da ƙunci a yanzu.
Tsohon jigon jam'iyyar APC ya soki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da cewa tsare-tsarenta kamar cire tallafin mai da faɗuwar darajar Naira ne suka jawo halin da ake ciki.
A cewarsa, galibin manufofin tattalin arziki da gwamnatin APC ta ɗauka ba su haifar da wani sakamako mai kyau ba, face yunwa da kunci ga ƴan Najeriya.
Tsohon jigon APC ya caccaki Bola Tinubu
Modibbo ya soki shugaban ƙasa Bola Tinubu da jefa ‘yan kasa cikin kunci ta hanyar manufofinsa da kuma zargin nuna bambanci wajen nada mukamai.
Tsohon jigo a jam’iyyar APC ya kuma yi Allah wadai da dokar sauya tsarin haraji, yana mai cewa kudirin ya fifita wasu bukatu fiye da jin dadin ‘yan Najeriya.
Ya yi iƙirarin cewa halin da mutane ke ciki na wahala ya nunka fiye da sau 10 daga halin wahalar da aka shiga a karkashin mulkin Muhammadu Buhari.
Mutane na wahala fiye da na mulkin Buhari
“Halin da ake ciki yanzu ya ninka sau 10 fiye da lokacin shugaba Buhari, sannan kuma, (shugaban ƙasa, Bola Tinubu) ya bai wa mutanen yankinsa manyan mukamai kamar ma’aikatun kudi, tattalin arzikin teku, da bankin CBN.
"Duk waɗannan muƙamai masu gwabi sun kasance a hannun Yarbawa, wanda hakan wata alamar tambaya ce kan ikirarin da shugaban kasa ke yi na cewa shi ɗan dimokradiyya ne,” in ji shi.
Sanatan PDP a Delta ya koma jam'iyyar APC
A wani labarin, kun ji cewa sanata mai wakiltar Delta ta Arewa a Majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ned Nwoko ya fice daga PDP zuwa APC.
Sanatan ya sanar da ficewarsa daga PDP ne mahaifarss a Idumuje Ugboko, da ke ƙaramar hukumar Aniocha ta Arewa a jihar Delta a ranar Talata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng