Yana Tare da Kwankwasiyya: Sani Danja ya Fito Takarar Shugaban Karamar Hukuma?

Yana Tare da Kwankwasiyya: Sani Danja ya Fito Takarar Shugaban Karamar Hukuma?

  • Shugaban hukumar tace fina-finai na jihar Kano, Abba El-Mustapha ya saki wasu zafafan fastocin takarar jarumi Sani Danja
  • Abin da fastocin ke nuna shi ne Sani Danja yana neman takarar kujerar shugaban karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano
  • Wannan na zuwa ne bayan da wasu mawaka da 'yan Kannywood suka fice daga tafiyar Kwankwasiyya, tare da komawa APC

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Siyasar jihar Kano ta sake daukar sabon salo yayin da aka ga fastocin fitaccen mawakin Hausa kuma jarumi a Kannywood, Sani Danja.

Fastocin Sani Danja sun karade shafukan sada zumunta, inda suka nuna cewa jarumin yana neman takara ta kujerar shugaban karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

Kara karanta wannan

Sauya Sheka: Rukunin mutane 3 da suka juyawa Abba Gida Gida da NNPP baya a watan nan

Fastocin neman takarar ciyaman na Sani Danja sun karade shafukan intanet
Abba El-Mustapha ya yi godiya ga matasan Nasara saboda kiran Sani Danja ya yi takara. Hoto: @abbaelmustaph1
Asali: Twitter

Fastocin Sani Danja sun shiga duniya

Shugaban hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano, Abba El-Mustapha ne ya wallafa hotunan a shafinsa na X a safiyar ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma bisa ga abin da El-Mustapha ya rubuta a shafinsa, ya nuna cewa matasan karamar hukumar Nasarawa ne suka yi kira ga Sani Danja ya fito takarar.

Da alama ba wai shi fitaccen tauraron ne ya bayyana hakan a hukumance ba.

Abba El-Mustapha ya wallafa cewa:

"Sani Danja 2024
"Matasan karamar hukumar Nasarawa, jihar Kano, Alhaji Sani Danja yana godiya da wannan kira. Allah Amin."

Kalli hotunan fastocin a nan kasa:

Takarar Danja: Mutane sun yi martani

@MuzzammilAdamu2:

"Muna masa fatan Alkairi. Amma kuma matsalar daya dan majalisar tarayya, Hassan Hussain daga Tudun Wada yake shi ma kuma Sani Musa danja dan Tudun Wada ne.

Kara karanta wannan

Kano: Siyasar Abba ta samu kalubale, fitattun yan Kannywood sun koma APC

@ad_nafiu:

"Mu ne Nassarawa kuma muna alfahari da hakan wallahi."

@Sadimr_real:

"Namu ya samu, muna yin tafiyar. A Nassarawa in dai mutum ba dan Birged ba ne ba za muyi shi ba zaben shugaban karamar hukuma."

@Bellogwd1:

"Masha Allahu, Dai dai hakan nake son gani. Allah ya sa ayi cikin nasara. Amin."

@HonAbdullahiM12

"AlhamuliLah.
"Sani Musa Danja har yanzu yana Kwankwasiyya."

'Yan Kannywood sun koma APC

Tun da fari, mun ruwaito cewa wasu fitattun jaruman Kannywood sun kara ficewa daga tafiyar gwamna Abba Kabir Yusuf suka koma APC.

Jam'iyyar APC ta nuna maraba da shigowar jaruman ta kuma fadi yadda za su cigaba da aiki wajen cimma burinsu a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.