Jerin sunayen Jaruman Kannywood uku da suka fito takara da kujerun da suke nema a 2023

Jerin sunayen Jaruman Kannywood uku da suka fito takara da kujerun da suke nema a 2023

  • Wasu daga cikin Jaruman Kannywood da tauraruwarsu ke haskawa sun bayyana tsayawa takarar siyasa a zaɓen 2023
  • Mun tattaro muku waɗan nan jaruman da suka nuna sha'awar ba da gudummuwarsu a ɓangaren shugabancin al'umma a Najeriya
  • Jarumi Ahmad Lawan wanda ya shirya shiri mai dogon Zango 'Izzar So' na cikin waɗan da ke neman takara

Jaruman masana'antar shriya fina-finan Hausa Kannywood ba'a barsu a baya wajen tsayawa takara yayin ake tunkarar babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Legit.ng hausa ta tattaro muku wasu Jarumai maza guda uku da Furodusa ɗaya na Kannywood waɗan da tauraruwarsu ke haskawa kuma suka ayyana tsayawa takara a mazaɓun su.

Bayanai sun nuna cewa da yuwuwar siyasar 2023 ta raba kan yan Kannywood zuwa gida biyu, rahoton da mafi yawan jaruman suka musanta.

Jaruman Kannywood.
Jerin sunayen Jaruman Kannywood uku da suka fito takara da kujerun da suke nema a 2023 Hoto: @Lawanahmad Yusufsaseen
Asali: Instagram

1. Furodusan IZZAR SO, Lawan Ahmad

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Wani Kazamin Hari Jihar Arewa, Sun Kashe Basarake

Mashiryin shiri mai farin jini kuma mai dogon Zango 'Izzar So' Lawan Ahmad ya bayyana tsayawa takarar ɗan majalisar jiha mai wakiltar Bakori a jihar Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jarumin wanda aka fi sani da Umar Hashim, sunan da ya ke amsawa a shirin Izzar So, ya sanar da tsayawa takara ne karkashin inuwar ham'iyyar APC.

Wani rubutu mai ɗauke da Hoton Fasta da ya saka a shafinsa na Instagram, Lawan Ahmad, ya ce ya miƙa wa Allah lamarinsa kuma a wurinsa ya ke nema.

Da wakilin Legit.ng Hausa ya tuntubi Jarumi Lawan Ahmad ta wayar salula, ya fara da shaida mana tarihin shigarsa siyasa, inda ya ce:

"Na fara ne da takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Bakori da Ɗanja, amma aka zauna da manya aka ce ya kamata na tafi majalisar jiha, ita ma ba'a samu an nema ba."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kaiwa Ayarin Dakarun Yan Sanda Hari a Arewa, An Rasa Rayuka

"Sai kuma wannan karan, kasan duk wanda ya hito takara ba yin kansa bane, jama'a ne suke kira a fito, shiyasa muka sake fitowa mu sake jarabawa."

2. Yusuf Saseen (Lukman na shirin Labarina)

Jarumi Yusuf Saseen, wanda mabiya Kannywood suka fi sani da Lukman ya tabbatar da tsayawa takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kano Municipal.

Lukman wanda tauraruwarsa ta haska a cikin shirin Labarina mai dogon zango, ya shaida wa wakilin Legit.ng hausa ta wayar salula cewa abokansa ne suka ga ya dace ya nemi takara.

Jarumi Yusuf ya ƙara da cewa a tarihin siyasarsa ya raka mutane da yake tsammanin na kirki ne, amma bai taɓa yin jam'iyyar APC ko PDP.

A zantawarsa da wakilin mu, Lukman wanda ya fito takara karkashin PDP ya ce:

""Eh dagaske ne zan yi takara, amma abokaina a Masana'anta da na rayuwar yau da kullum ne suke ganin ya dace duba da kila suna ganin ingancin jagoranci a wuri na."

Kara karanta wannan

Dubbannin Malaman Makaranta a Arewa Sun Yunkuro, Sun Ayyana Wanda Zasu Goyi Baya a 2023

3. Ali Rabiu Ali (Daddy)

Jarumi, Furodusa kuma Darakta a masana'antar Kannywood, Ali Rabiu Ali, ya tabbatar da tsayawa takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Dala a Kano.

A wata Fasta da jarumin ya saki a shafinsa na Instagram , Ali wanda aka fi sani da Daddy ya nuna cewa yana fatan ya zama magajin Malam Aminu Kano.

Jarumin ya bayyana cewa shi jikan Malam Aminu Kano ne kasancewar shi ne wanda ya haifi mahaifiyarsa, sai dai a bayaninsa ya ce yan siyasar yanzu sun bar turbar da kakansa ya ɗora su.

Ya ce:

""Ina fatan ɗorawa daga inda ya tsaya da yardar Allah kuma da karfin ikon Allah domin na yi bakin kwarkwardo a ɓangaren wakilci. Idan zan zama Alkairi ga al'ummar Dala Allah ya sani."

4. Naziru Ɗanhajiya

Furudusa a Kanywood, Naziru Auwal Yadakwari wanda aka fi sani da Dan Hajiya ya sanar da fitowa takarar ɗan majalisar jiha mai wakiltar Kura/Garum Malam karkashin APC.

Kara karanta wannan

Rikicin APC Ya Dauki Sabon Salo, Majalisa Ta Tsige Ciyaman Daga Mukaminsa a Jihar Arewa

Da yake bayyana aniyarsa a zaɓen 2023, Ɗan Hajiya ya nuna wa duniya cewa ya sayi Fom ɗin takara na jam'iyyar APC.

A wani labarin kuma Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya bayyana sunan ɗan takarar da yake rokon Allah ya gaji Buhari a 2023

Fitaccen Malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ɗahiru Bauchi, ya nuna goyon bayansa ga Yemi Osinbajo a zaɓen 2023.

Malamin ya ce ya jima ya na wa mataimakin shugaban Addu'a don haka zai nunka rokon Allah ya samu nasara a zaɓe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel