Sani Danja ya bude katon kamfanin sayar da motoci a birnin Abuja

Sani Danja ya bude katon kamfanin sayar da motoci a birnin Abuja

- A yayin da kowanne jarumi yake kokarin ta kai ta kai domin ganin ya kafa sana'ar da za ta zame mishi madogara a nan gaba

- Jarumi Sani Danja ya bude wani katafaren kamfanin sayar da motoci a babban birnin tarayya Abuja

- Wannan dai na zuwa ne makonni kadan bayan hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta garkame masa wurin daukar hoto

Kamar yadda kuka sani a yanzu kaka ce ga 'yan fim na bude sana'o'in da zasu rika jarrabawa bayan sana'arsu ta fim, inda kusan daidaiku ne daga manyan jaruman masana'antar basa yin irin wannan dabara ta bude sana'ar kota kwana.

Kamar yadda a kwanakin baya jarumi Ali Nuhu ya bude shagon sayar da kaya, haka ita ma jaruma Maryam Yahaya, sannan ita kuma Sadiya Kabala ta bude shagon sayar da takalma da kuma sana'ar kiwon kifi.

Sani Danja ya bude katon kamfanin sayar da motoci a birnin Abuja
Sani Danja ya bude katon kamfanin sayar da motoci a birnin Abuja
Asali: Facebook

Haka shi ma jarumi Sani Danja ya bude shagon daukar hoto, inda ita kuma Rahama Sadau a kwanan nan ta bude sabon gidan sayar da abinci banda kamfanin jambakin ta da shagon mai da tsohuwa yarinya, sai kuma jaruma Hadiza Gabon da Maryam Booth da suka jima suna gwada 'yan sana'o'in su na shagon kwalliya da sauran su.

Sani Danja wanda dama tun kafin masana'antar ta fara walagigi dama ba a cika ganinshi a cikin fina-finai ba, inda wasu ke ganin al'amuran siyasa da kuma kudi da ya samu su suka saka ya watsar da harkar, wasu kuma na ganin kawai an daina yi da shi ne, duk da kasancewar shi jigo a cikin masana'antar.

Jim kadan bayan hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta garkame masa shagon hoto ta kuma bude bayan wasu 'yan kwanaki, jarumin ya bayyana sabon kamfani da ya bude na sayar da manyan motoci, inda har ya wallafa rijistar da ya yiwa kamfanin, sannan kuma ya sanya samfurin motocin da yake siyarwa.

Ofishin sayar da motocin jarumin dai yana unguwar Wuse 2 dake garin Abuja.

Muna fatan Allah yasa albarka a sana'ar ya kuma karo arziki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel