Kannywood: Jarumi Lukman na Shirin Labarina ya fito takarar siyasa a jihar Kano

Kannywood: Jarumi Lukman na Shirin Labarina ya fito takarar siyasa a jihar Kano

  • Yayin da zaɓen 2023 ke ƙara ƙaratowa, yan Najeriya dake da niyyar tsayawa takara na cigaba da faɗa wa duniya aniyarsu
  • A masana'antar Kannywood, Jarumi Lukman na Labari na ya bayyana tsayawa takarar ɗan majalisar tarayya daga Kano
  • Yusuf Saseen zai nemi takara karkashin inuwar PDP, kuma ba shi ne na farko da ya fito takarar siyasa ba a Kannywood

Kano - Jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa, Yusuf Saseen, wanda jama'a suka fi sani da Lukman na shirin Labarina Series, ya tsaya takarar siyasa a Kano.

A wani rubutu da abokin Jarumin kuma Darakta a Kannywood, Sulaiman Bello Easy, ya saki a shafinsa na Instgaram, ya nuna Jarumin zai nemi takara ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP.

Jarumi Yusuf Saseen wato Lukman.
Kannywood: Jarumi Lukman na Shirin Labarina ya fito takarar siyasa a jihar Kano Hoto: @Yusuf_saseen
Asali: Instagram

A fastar takara da ta karaɗe shafin Instgaram, Lukman Na Labarina, ya tsaya takarar dan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Kano Municipal a zaɓen 2023 dake tafe.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

Darakta Sani Easy ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duk da ba na siyasar PDP amma dole na yi wa abokina kara na tallata shi saboda ingancinsa da sanin mutuncin al'umma, bana jin ko a wace jam'iyya ya fito zan ƙasa hidimta masa."
"Duba da gudummuwar da yake bai wa al'umma ta kowane ɓangare, a gaskiya ya cancanta, muna barar kuri'un ku da kuma fatan Nasara."

Waye Yusuf Saseen?

Ciakkken sunansa shine, Yusuf Muhammad Abdullahi, amma an fi saninsa da Yusuf Saseen, haifaffen jihar Kano ne wanda ya ta so a cikin jihar, ya yi karatun Firamare da Sakandire a Kano.

Fitaccen Jarumin, wanda ya shahara bisa rawar da yake takawa a shirin 'Labarina mai dogon Zango' a matsayin ɗaya daga cikin Samarin Sumayya, ɗan asalin Anguwar gini ne ta cikin garin Kano.

Bayan kammala karatun Digirinsa a Jami'ar Bayero, Lukman ya yi aikin bautar ƙasa NYSC a jihar Nasarawa, daga bisani ya shiga harkar shirya fina finai ta Kannywood.

Kara karanta wannan

Mun cika alkawuran da muka yiwa yan Najeriya a dukkan bangarori, musamman gidaje: Buhari

Legit.ng Hausa. ta tuntuɓi Yusuf Saseen Wato Lukman ta wayar salula kan shirinsa na neman wannan takara, kuma ya faɗa wa wakilinmu cewa:

"Eh dagaske ne zan yi takara, amma abokaina a Masana'anta da na rayuwar yau da kullum ne suke ganin ya dace duba da kila suna ganin ingancin jagoranci a wuri na."
"Abun ya samo asali ne daga wasu abubuwa da suke faruwa a ƙasa, tun daga tsaro rai ya zamo ba komai ba, ruwa sai ka siya a gari kamar Kano, wuta ma ba'a maganarta, to mun rasa inda wakilci ke tafiya."
"Tun daga 1999 zuwa yau kullum abun ƙara lalacewa yake, wuta da ruwa sun zama abin da ake yaƙin neman zaɓe da su, yanzu da tsaro ake neman zaɓe."

Meyasa ya zaɓi neman takara a PDP?

Jarumi Yusuf ya ƙara da cewa a tarihin siyasarsa ya raka mutane da yake tsammanin na kirki ne, amma bai taɓa yin jam'iyyar APC ko PDP.

Kara karanta wannan

Manyan jaruman Kannywood 5 da suka yi tashe a farkon 2000

A cewarsa, tun da daɗewa yana siyasa a jam'iyyar PRP, ya yi a jiharsa Kano da kuma Bauchi kuma sannan ya yi jam'iyyar PDM.

"A gogayyar siyasa na gano cewa mutanen kirki ba su samun dama a manyan jam'iyyu, sai kana da uban gida. Na yi jam'iyyu da ba su shahara ba, amma kowaye zan zaɓa sai ya gaya mun me zai wa al'umma."
"Na shiga PDP ne saboda a da tana da karfi amma fitar Kwankwaso ya rage mata karfi, mutane na ganin ba zata yi kataɓus ba. Ba zan iya siyasar Uban gida ba, sai ka shiga can ka roƙa ka yi biyayya."
PDP ake ganin ta zama saniyar ware, kowa na ganin APC ko NNPP ce zasu ci, to ni kuma ina son a bani takara bisa cancanta, hakan yasa na koma PDP."

Ya kuma yi kira ga al'umma su jingine siyasar kudi da ta Uban gida, su rungumi cancanta domin su zabi jagorori nagari. A cewarsa mutanen kirki na gefe.

Kara karanta wannan

Kotu ta bada umurnin garkame matasa biyu kan laifin 'ba haya' cikin Masallaci

A wani labarin kuma Farin Jakada: Jarumin Kannywood Lawan Ahmad ya fito takarar siyasa a jihar Katsina

Jarumin Kannywood, Lawan Ahmad, ya tabbatar da shiga tseren takarar mamba mai wakiltar Bakori a majalisar dokokin Katsina.

Jarumin wanda tauraruwarsa ke haskawa a shirin Izzar So da sunan Umar Hashim, ya fito siyasar ne karkashin jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel