Kwankwaso Ya Barar, Dan Takarar Gwamna Ya Yi Murabus a Gombe, Ya Tura Sako

Kwankwaso Ya Barar, Dan Takarar Gwamna Ya Yi Murabus a Gombe, Ya Tura Sako

  • Jagoran jam'iyyar NNPP kuma dan takarar gwamnan jihar Gombe, Hon. Khamisu Mailantarki ya yi murabus
  • Mailantarki ya sanar da yin murabus din ne a yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024 a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu
  • Legit Hausa ta ji ta bakin sakataren jam'iyyar a Gombe, Muhammad Baba Sherrif kan wannan murabus na Mailantarki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Jam'iyyar NNPP ta tafka babban rashi bayan dan takarar gwamnanta daga jihar Gombe ya yi murabus.

Jagoran jam'yyar a Gombe kuma dan takarar gwamna, Hon. Khamisu Mailantarki ya sanar da yin murabus daga jam'iyyar.

Dan takarar gwamna a NNPP ya fice daga jam'iyyar
Dan takarar gwamnan Gombe a jam'iyyar NNPP, Hon. Mailantarki ya yi murabus. Hoto: Hon. Khamis Mailantarki, Rabiu Musa Kwankwaso.
Asali: Facebook

Jigon NNPP ya yi murabus daga jam'iyyar

Kara karanta wannan

PDP ta sake rikicewa yayin da ta dakatar da na hannun daman Wike, ta jero dalilai

Jigon jam'iyyar kuma tsohon dan takarar shugabancin karamar hukumar Gombe, Adamu Babale Makera shi ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Murabus din Mailantarki na kunshe ne a cikin wata wasika da ya sanyawa hannu a yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024.

A cikin wasikar, Mailantarki ya yi godiya ga shugabannin jam'iyyar game da damar da suka ba shi wurin gina siyasarsa.

Har ila yau, ya kuma mika godiya ga sauran mambobin jam'iyyar da suka nuna masa goyon baya musamman a takarar zaben 2023.

Mailantarki ya yi godiya ga jam'iyyar NNPP

"Ina mai sanar da ku cewa na yi murabus a matsayin mamban jam'iyyar NNPP daga yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024."
"Kasancewa da ku da sauran mambobin jam'iyyar abin alfahari ne wanda ya yi matukar tasiri a siyasa ta, ina godiya da damar da kuka ba ni."

Kara karanta wannan

Rashin aikin yi: Ganduje ya ba matasa shawarar abin da za su yi bayan kammala karatu

"Ina matukar godiya ga shugabanni da mambobin jam'iyya da goyon baya da suka nuna min a takarar 2023 na neman gwamnan jihar Gombe."

- Khamisu Mailantarki

Legit Hausa ta tattauna da sakataren jam'iyyar

Legit Hausa ta ji ta bakin sakataren jam'iyyar a Gombe, Muhammad Baba Sherrif kan wannan murabus din Mailantarki

Ya ce tabbas sun yi rashin jigo inda ya ce babu jam'iyyar da ba za ta so ya kasance tare da ita ba.

"Rashin jigo irin Hon. Mailantarki rashi ne da duk wanda ya san siyasa ba zai ji dadi ba, daga lokacin da na iske takardan murabus dinsa, wallahi kai kace mutuwa aka min."
"Domin Mailantarki cikakken dan siyasa ne da babu jam'iyyar da ba za ta so kasancewarsa cikinta ba."
"Amma ya zama wajibi mu mutunta ra'ayinsa tare da yi masa fatan alkairi a duk inda zai samu kansa, muna addu'ar Allah ya sa ficewar ta zama alkairi."

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya fara samun koma baya, shugabannin NNPP sun koma APC

- Muhammad Baba Sherrif

Edo: NNPP ta karbi sabbin tuba 2,000

A wani labarin, kun ji cewa Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben jihar Edo, jami'yyar NNPP ta karbi sabbin tuba daga wasu jam'iyyu.

Dan takarar gwamnan jihar, Fasto Azehme Azena shi ya karbi sabbin tuban yayin tattakin zaman lafiya a ranar Alhamis 27 ga watan Yunin 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.