Ondo 2024: PDP Ta Gamu da Babbar Matsala, Jam’iyyu 74 Marasa Rijista Sun Goyi Bayan APC
- Jam'iyyar PDP ta gamu da matsala a jihar Ondo bayan da jam'iyyu 74 karkashin kungiyar CDPPN suka koma bayan Lucky Aiyedatiwa
- CDPPN, kungiya ce ta jam’iyyun siyasa da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta soke rajistarsu saboda wasu dalilai
- Jagoran kungiyar jam'iyyun siyasar, William Olu-Aderounmu ya ce za su goyi bayan jam'iyyar APC a zaben Ondo na ranar 16 ga Nuwamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Ondo - Jam’iyyun siyasa 74 a karkashin inuwar kungiyar jam’iyyun siyasar Najeriya marasa rijista (CDPPN), sun ruguza tsare tsarensu tare da hadewa waje daya.
An ce jam'iyyun sun hade waje daya ne domin goyawa jam'iyyar APC baya a zaben gwamnan Ondo da za a yi ranar 16 ga Nuwamba, 2024.
Jam'iyyu 74 sun goyi bayan APC
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa CDPPN kungiya ce ta jam’iyyun siyasa da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta soke rajistarsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
William Olu-Aderounmu, wanda ya jagoranci kungiyar a wata ganawa da Gwamna Lucky Aiyedatiwa a Akure, ya ce gwamnan ya mallaki dukkanin abubuwan da ake da bukata domin kai jihar zuwa mataki na gaba.
Olu-Aderounmu ya ce ayyukan da Lucky Aiyedatiwa ke gudanarwa a fadin jihar ne ya sa jam'iyyun CDPPN suka yi mubayi'a a gare shi, in ji rahoton TVC News.
APC ta yi wa jam'iyyun CDPPN albishir
A nasa jawabin, kodinetan CDPPN na jihar Ondo, Rotimi Akindejoye, ya yabawa gwamnan bisa yadda yake gudanar da ayyukansa da salon jagoranci a jihar.
Wakilin mutane masu bukata ta musamman, Elegbeleye Sanmi, ya yabawa gwamnan bisa shigar da mambobinsu a kowane shiri da ayyukan gwamnatin jihar.
Da yake martani, gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Olayide Adelami, ya ba kungiyar CDPPN tabbacin sanya ta a cikin tsare-tsaren APC na dukkanin matakai.
Ma'aiktan jami'a sun ba gwamnti wa'adi
A wani labarin, mun ruwaito cewa ma'aikatan jami'o'in Najeriya karkashin kungiyoyin NASU da SSANU sun sha alwashin rufe jami'o'in kasar saboda gwamnati ta rike albashin 'ya 'yansu.
Ma'aikatan sun nemi gwamnatin ta biya albashin nan da mako biyu ko kuma ta ga fushinta a zahirance wanda zai hada da rufe jami'o'in da ke fadin kasar .
Asali: Legit.ng