Zaben Fitar da Gwani: An Aike da Sako Mara Daɗi Ga Shugaba Tinubu Kan Gwamnan APC

Zaben Fitar da Gwani: An Aike da Sako Mara Daɗi Ga Shugaba Tinubu Kan Gwamnan APC

  • Wasu shugabannin APC a jihar Ondo sun zargi Gwamna Lucky Aiyedatiwa da aikata babban laifi gabanin zaɓen fitar da ɗan takara
  • Daga cikin abubuwan da suka zargi gwamnan, jagororin APC sun yi iƙirarin cewa Aiyedatiwa ya fara buga katunan zama mamban jam'iyya na bogi
  • Amma kwamitin yaƙin neman zaben gwamnan ya musanta zarge-zargen, inda ya ce wasu ƴan takara ne suka kirkiri labarin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Wasu jagororin jam'iyyar APC mai mulki a jihar Ondo sun nuna damuwa kan zargin cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa na ƙulla wata manaƙisa.

Jiga-jigan karkashin wata ƙungiyar rajin tabbatar da shugabanci na gari, sun zargi gwamnan da kokarin jirkita zaben fitar da gwani na APC da za a yi ranar 20 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Tsohon dan takarar shugaban kasar Nijeriya, Ogbonnaya Onu ya rasu

Gwamna Lucky Aiyedatiwa.
Gwamnan Ondo ya musanta zargin da ake masa Hoto: Hon.Lucky Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Shugaban ƙungiyar, Evangelist Tade Ojo, ya koka kan lamarin a wata sanarwa da ya aike ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Tribune Nigeria ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aiyedatiwa na shirya maguɗi a APC?

A cewarsa, Gwamna Aiyedatiwa tare da magoya bayansa sun fara buga katunan jam'iyya na bogi domin rabawa wasu mutane da ba mambobin jam'iyyar APC ba.

Mista Ojo ya ce:

"Muna amfani da wannan damar wajen kira ga uwar jam'iyyar APC ta ƙasa da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu su takawa Gwamna Aiyedatiwa birki daga shirinsa na wargaza zaben fitar da gwani.
"Muna kuma kira ga shugabannin jam'iyyar mu su dakatar da shi daga shirinsa domin ka da ya gurɓata damar da APC ke da ita a zaben gwamnan da za a yi a watan Nuwamba.
"Jihar Ondo tana gaba da kowa har da shi kansa Gwamna Aiyedatiwa, mu na da yaƙinin sun fara shirin gurɓata madarar matuƙar ba za su samu ba."

Kara karanta wannan

Shugabanci: An faɗi wanda ya cancanci zama sabon shugaban jam'iyyar PDP daga Arewa

Gwamnan ya musanta zargin

Sai dai a ɗaya ɓangaren, kwamitin kamfen Gwamna Aiyedatiwa (LACO-FS) ya yi fatali da wannan zargin da cewa wasu marasa alƙibla ne suka kirkiro zargin.

LACO-FS ya yi iƙirarin cewa Aiyedatiwa ya yi nisa da wannan ƙaryar na buga katunan jam'iyya na bogi kamar yadda ake zargi, rahoton jaridar Independent.

APC ta shirya lashe zaɓen Ondo

A wani rahoton kuma Abdullahi Umar Ganduje wanda shi ne shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya yi magana kan zaɓen jihar Ondo da yake tafe.

Dr. Ganduje ya yi nuni da cewa jam'iyyar ce za ta yi nasara a zaɓen gwamnan jihar na watan Nuwamba mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel