Tsohon Shugaban APC Ya Fallasa Wanda Ya Jawo Ake Binciken Gwamnatin El Rufai
- Salihu Muhammad Lukman ya na ganin babu inda Bola Ahmed Tinubu da Uba Sani za su kara motsawa a tafiyar siyasa
- Tsohon mataimakin shugaban na APC yana ganin fadar shugaban kasa tana da hannu wajen binciken Nasir El-Rufai a Kaduna
- A wata wasika, Salihu Muhammad Lukman ya fadawa gwamnan Kaduna cewa an kama hanyar ganin bayan mulkinsu a 2027
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kaduna - Salihu Muhammad Lukman ya yi kaca-kaca da gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, har ya ce ba zai zarce a ofis ba.
Tsohon mataimakin shugaban na jam’iyyar APC yana ganin Bola Tinubu da Uba Sani ba za su yi nasarar komawa kujerunsu a 2027 ba.
Lukman ya kare gwamnatin El-Rufai
The Guardian ta rahoto Salihu Muhammad Lukman yana magana a kan rikicin da Mai girma gwamna Uba Sani yake yi da Nasir El-Rufai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan siyasar yana ganin cewa gwamnan Kaduna yana taya fadar shugaban kasa yakar tsohon gwamnan ne da sunan binciken mulkinsa.
A wata wasika da ya rubuta a ranar 13 ga watan Yuni, Salihu Lukman ya ce tun yanzu an fara shirin kifar da Tinubu da gwamnatin Uba.
Watakila APC za ta rasa zaben 2027
A takardar, Lukman ya gargadi Uba Sani, ya ce ko da ya dace, shekaru bakwai suka rage masa kamar yadda Daily Post ta rahoto a jiya.
Idan har APC ba ta shiga taitayinta ba, ‘dan siyasar ya ce za su yi bakin kokarinsu wajen ganin sun ga bayan jam’iyyar a takarar 2027.
Vanguard ta rahoto Lukman yana zargin Ibrahim Zailani da hannu a binciken gwamnatin El-Rufai tare da taimakon fadar shugaban kasa.
Wadanda aka aikawa wasikar sun hada Mallam Nasir El-Rufai, Ramalan Yero, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, B. A. Law-al da Hon. Garba Datti.
Haka kuma an hada da Suleiman Hunkuyi, Yusuf Mairago, Lawal Samaila Yakawada, Bashir Abubakar Alhaji da Mohammed Sani Dattijo.
Uba Sani da gwamnatin Nasir El-Rufai
Ana da labarin ana ganin gwamnatin Uba Sani ta taso Nasir El-Rufai a gaba duk da alakar da ke tsakanin mutanen da suke tsofaffin abokai.
Shehu Usman Adamu bai ganin rigima ake yi a Kaduna, ya ce gwamna da mai gidansa aminai ne har yau, sunnar siyasa ta gaji haka.
Asali: Legit.ng