Ana Dab da Zabe, ’Yan Sanda Sun Kama Kakakin Yakin Zaben Gwamnan PDP, an Gano Dalili

Ana Dab da Zabe, ’Yan Sanda Sun Kama Kakakin Yakin Zaben Gwamnan PDP, an Gano Dalili

  • ‘Yan sanda sun kama mataimakin daraktan yada labarai na jam’iyyar PDP a yakin neman zaben gwamnan Edo, Rabaran Olu Martins
  • Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Funsho Adegboye ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Talata, 11 ga watan Yuni
  • Kwamishinan ‘yan sandan ya ce kalaman kakakin yakin neman zaben PDP na tunzurar da jama'a, kuma an gurfanar da shi a gaban kotu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benin, jihar Edo - An kama mataimakin daraktan yada labarai na jam’iyyar PDP a yakin neman zaben gwamnan Edo, Rabaran Olu Martins.

'Yan sanda a Edo sun cafke kakakin yakin neman zaben gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP
'Yan sanda sun kama kakakin jam'iyyar PDP a Edo. Hoto:Rev Olu Martins
Asali: Twitter

Edo 2024: An kama kakakin PDP

An ce rundunar ‘yan sandan Edo ce ta kama Rabaran Martins kan zargin furta kalaman batanci da tunzura jama'a, kuma ta gurfanar da shi gaban kotu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kara samun nasara, an harbe 'yan ta'adda a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Funsho Adegboye ne ya bayyana hakan a Benin, babban birnin jihar Edo a ranar Talata kamar yadda rahoton PM News ya nuna.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, ya kara da cewa furucin kakakin yakin neman zaben jam'iyyar PDP na iya haifar da tashin hankali a Edo.

APC ta nemi kama mai magana madadin PDP

Tun da fari, jaridar Leadership ta ruwaito cewa jam’iyyar APC ta bukaci ‘yan sanda da su kama kakakin yakin neman zaben gwamnan PDP, Rev Olu Martins kan furta kalaman batanci.

A wata sanarwa da ya fitar a Benin, shugaban jam’iyyar APC, Jarret Tenebe ya ja hankalin jami'an tsaro kan zargin da ake yiwa PDP na tayar da zaune tsaye gabanin zaben jihar.

Zaben Edo: An gargadi 'yan siyasa

Kara karanta wannan

Babbar kotu ta yanke hukunci kan tsige ƴan majalisa 27 da suka sauya sheƙa zuwa APC

Kwamishinan ‘yan sandan jihar na Edo, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki a jihar mai arzikin man fetur da su yi siyasarsu bisa ka’ida.

Adegboye ya gargadi ‘yan siyasar jihar da su guji yin wani abu da zai iya haifar da tashin hankali a jihar ko kuma karfafa gwiwar jama’a wajen aikata laifuffuka.

Gwamna ya garkame kamfanin lantarki

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Enugu ta garkame hedikwata da ofisoshin kamfanin rarraba wutar lantarkin Enugu da aka fi sani da EEDC.

Wannan na zuwa ne makonni bayan kamfanin EEDC ya aika wa gwamnatin jihar sanarwar datse wutar lantarki da ta shiga gidan gwamnatin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.