"Ina Fatan Lafiya": Atiku Ya Magantu Bayan Tinubu Ya Zame Har Kasa a Faifan Bidiyo

"Ina Fatan Lafiya": Atiku Ya Magantu Bayan Tinubu Ya Zame Har Kasa a Faifan Bidiyo

  • Yayin da ake ta yaɗa faifan bidiyon Shugaba Tinubu lokacin da ya zame a Eagle Square, Atiku Abubakar ya yi martani
  • Ɗan takarar shugaban kasa PDP ya nuna damuwa da alhini kan abin da ya faru da shugaban a yau Laraba 12 ga watan Yuni
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani masoyin Atiku Abubakar kan wannan jaje na dan takarar shugaban kasa ga Tinubu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya magantu bayan Bola Tinubu ya zame yayin bikin dimukradiyya.

Atiku ya jajantawa Tinubu dangane da zamewar inda ya ce yana fatan shugaban yana cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya bayyana yadda Tinubu ya gina Atiku da sauran mutane a siyasa

Atiku ya magantu bayan Tinubu ya zame a taro
Atiku ya jajantawa Tinubu bayan zamewa a taron dimukradiyya. Hoto: Sean Gallup/Kola Sulaimon.
Asali: Getty Images

Atiku ya jajantawa Tinubu bayan ya zame

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka a shafinsa na X da bidiyon abin da ya faru a yau Laraba 12 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina jajantawa Shugaba Tinubu dangane da hatsarin da ya afku da shi yayin da yake ƙoƙarin zagaya masu fareti ranar dimokaraɗiyya.
"Ina dai fatan yana lafiya, babu wata matsala."

- Atiku Abubakar

Dimukradiyya: Tinubu ya zame a taro

Wannan na zuwa ne bayan an yaɗa wani faifan bidiyo da shugaban ya zame yayin da yake hawa matakalar mota yayin bikin.

An gudanar da bikin ne a dandalin 'Eagle Square' da ke birnin Abuja domin murnan ranar dimukradiyya a Najeriya.

Wannan lamari ya tada kura tsakanin ƴan Najeriya inda wasu ke jajantawa shugaban yayin da wasu ke nuna jin dadinsu kan lamarin.

Kara karanta wannan

"Ba faɗuwa na yi ba" Bola Tinubu ya yi magana kan abin da ya faru a Eagle Square

Legit Hausa ta ji ta bakin wani masoyin Atiku Abubakar kan wannan jaje na dan takarar shugaban kasa ga Tinubu.

Kwamred Abubakar Aliyu ya ce Atiku ya yi dai-dai saboda ita siyasa ba gaba ba ce idan wani abu ya samu mutum dole za ka tausaya masa.

"Wasu suna ta ihu cewa jajen na karya ne, to wannan ai a zuciya ta ke babu wanda ya san gaibu."
"Atiku ya kasance mutum ne mai tausayi duk adawarsa yana kawar da siyasa idan har irin wannan abin ya faru."

- Abubakar Aliyu

Atiku ya magantu kan halin kunci

Kun ji cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakarya ɗora alhakin halin ƙuncin da ƴan Najeriya suke ciki kan jam’iyyar APC.

Atiku ya caccaki tsare-tsaren gwamnatin Bola Tinubu inda ya ce su suka jefa al'ummar kasar halin kunci da suke ciki a yanzu.

Kara karanta wannan

"Yar zamewa kawai ya yi," fadar shugaban kasa ta yi bayanin faduwar Bola Tinubu

Najeriya dai na fuskantar ƙalubalen taɓarɓarewar tattalin arziki, lamarin da ya sanya ƴan ƙasar ke matukar shan wahala wajen biyan buƙatun yau da kullum.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.