Atiku Abubakar ya Faɗi Hanya 1 da Za a Ceto Najeriya Daga Halin da ta Shiga

Atiku Abubakar ya Faɗi Hanya 1 da Za a Ceto Najeriya Daga Halin da ta Shiga

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya jaddada buƙatar jam'iyyun siyasa su yi haɗaka domin ceto Najeriya daga halin da ta ke ciki na matsin rayuwa
  • Atiku Abubakar, wanda ke zawarcin kujerar shugaban kasar Najeriya na ganin ba za a cimma ci gaban da ake bukata ba matukar jam'iyyun siyasa ba su hada hannu wuri guda ba
  • Jagoran na PDP ya bayyana haka ne lokacin da haɗakar ƙungiyar da ke goyon bayan PDP ta ziyarce shi domin jaddada goyon bayansu ƙarƙashin Anucha Katchy

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nemi haɗin kan jam'iyyun siyasa domin ceto Najeriya daga ƙangin da mulkin APC ya jefa ta. Atiku Abubakar, wanda ya yi takarar shugabancin kasar nan a zaɓen 2023 ya bayyana haka ne ga hadakar magoya bayan PDP da suka ziyarce shi domin jaddada goyon bayansu.

Kara karanta wannan

Neja: Abubuwan sun rikice a APC, an dakatar da shugabar mata a Arewa

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar ya nemi haɗaka domin kawo gyara Najeriya Hoto: @atiku
Asali: Twitter

A wani sako da mataimakin ɗan takarar kan kafafen yaɗa labarai, AbdulRasheed Shehu ya wallafa a shafinsa na facebook, shugaban haɗakar Anucha Katchy ya yaba da kishin ƙasar da Atiku Abubakar ke da shi. Ya ce ana sane da yadda tsohon mataimakin shugaban kasar ya jagoranci tawagar da ta yi dalilin yafewa Najeriya wasu basussuka da ake binta daga Paris Club.

Atiku: "70% mukaman gwamnati na matasa ne"

Ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa matasa da mata na daga wadanda ya fi kamata a tallafawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce matuƙar ya zama shugaban Najeriya, kaso 70% na mukaman gwamnati na matasa ne, yayin da zai bayar da $10bn ga masu kanana da matsakaitan sana'o'in mata zalla.

Sai dai Atiku Abubakar ya ƙara da cewa hakan ba zai tabbata ba sai an yi haɗaka mai ƙarfi domin kawar da APC daga mulkin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun nemi a mayar da wa'adi 1 ga shugaban ƙasa, sun faɗi adadin shekaru

Jagoran PDP ya kuma bayyana farin ciki matuka da hadakar kungiyar ta ziyarce shi, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

Atiku: "Ni na ceto siyasar Tinubu"

A wani labarin kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya musanta cewa Bola Tinubu ne ya cicciɓa shi a siyasar kasar nan.

Ya ce hasali ma shi ne ya yi faɗi tashin ceto siyasar Tinubu har ya iya zama gwamna a jihar Legas, don ba dan shi ba, da siyasar Tinubu ta zo ƙarshe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel