Tinubu Ya Faɗi Ƙasa Yayin Taron Ranar Dimokuraɗiyya, Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Martani

Tinubu Ya Faɗi Ƙasa Yayin Taron Ranar Dimokuraɗiyya, Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Martani

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fadi kasa yayin da yake kokarin hawa mota a yayin bikin ranar dimokuraɗiyya
  • Bola Tinubu ya fadi ne yayin da ake faretin murnar ranar dimokuraɗiyya a dandalin Eagle Square a birnin tarayya Abuja
  • Fadar shugaban kasa ta yi bayani kan lamarin inda ta ce ba abin tashin hankali ba ne tunda shugaba kasar ya cigaba da tafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta fadi kasa yayin da yake yunkurin hawa motar fareti a Abuja.

Shugaban kasar ya fadi ne a dandalin Eagle Square yayin da ake faretin murnar ranar dimokuraɗiyya a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Yar zamewa kawai ya yi," fadar shugaban kasa ta yi bayanin faduwar Bola Tinubu

Shugaba Tinubu
Fadar shugaban kasa ta ce ba matsala kan faduwar Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A bidiyon da Atiku Abubakar ya wallafa a shafinsa na Facebook an hango shugaban kasar ya fadi yayin da yake kokarin shiga motar faretin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya faru bayan Tinubu ya fadi?

A cikin bidiyon, bayan shugaba Bola Tinubu ya fadi, jami'an tsaro sun kewaye motar domin kokarin ba shi agajin gaggawa.

Amma duk da haka, shugaban kasar ya mike ya cigaba da tafiya kuma bikin ya cigaba da gudana kamar yadda aka tsara.

Fadar shugaban kasa ta yi martani

Legit ta tattaro cewa faduwar shugaban kasar ta tayar da kura a kafafen sadarwa inda jama'a da dama suka tofa albarkacin bakinsu.

Sai dai fadar shugaban kasa ta ce ba abu ba ne da ya kamata ya tayar da hankali musamman ma ganin shugaban kasar ya cigaba da komai lafiya.

Kara karanta wannan

"Ina fatan lafiya": Atiku ya magantu bayan Tinubu ya zame har kasa a faifan bidiyo

Faduwar Tinubu: Atiku ya yi magana

Babban abokin hamayyar Bola Tinubu, Atiku Abubakar ya shiga cikin wadanda suka yi martani kan faduwar shugaban kasar.

Atiku Abubakar ya yi martani cikin shaguɓe inda ya ce yana cikin alhini kan abin da ya samu shugaban kasar.

Tinubu ya yi magana kan albashi

A wani rahoton, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya shirya tura kudirin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata ga majalisar tarayya domin ta amince da shi.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da haka ne a jawabinsa na murnar ranar dimokuraɗiyya yau Laraba, 12 ga watan Yuni, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng