Zaben Gwamnan Edo: Sabon Rikici Ya Barke a PDP, an Samu Karin Bayani

Zaben Gwamnan Edo: Sabon Rikici Ya Barke a PDP, an Samu Karin Bayani

  • Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya sake tayar da tarzoma a ofishin mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na kasa da ke Abuja
  • Shaibu dai ya dage akan lallai shi ne ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar da aka gudanar a na kujerar gwamnan jihar Edo
  • Ya kuma yi barazanar maka jam'iyyar a gaban kotu ma damar taki bin ka'idojinta, lamarin da ya ƙara ta'azzara wutar rikicin da ta mamaye PDP

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Wani sabon rikici ya sake kunno kai a jam’iyyar PDP biyo bayan zaben fidda gwani na gwamnan jihar Edo da jam'iyyar ta kammala.

Mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu, ya dage cewa shi ne ya lashe zaben fidda gwanin kuma dole ne jam'iyyar ta ba shi takardar shaidar cin zaben.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamna ya ƙara tada rigima, ya dira sakateriyar PDP ta ƙasa kan muhimmin abu 1

Zaben Gwamnan Edo: Sabon Rikici Ya Barke a PDP
Zaben Edo: Shaibu ya dage a kan lallai shi ne ya lashe zaben fidda gwani na PDP. Hoto: @HonPhilipShaibu
Asali: Facebook

Shaibu, wanda ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani a wani tsagi na jam’iyyar, ya dira sakatariyar PDP ta kasa a jiya, inda ya bukaci a ba shi takardar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaibu ya yi barazanar maka PDP a gaban kotu

The Cable ta ruwaito cewa shugaban jam’iyyar PDP na Kasa, Amb. Umar Damagum ya ba Dokta Asue Ighodalo takardar shaidar lashe zaben a hukumance, lamarin da ya harzuka Shaibu.

Mataimakin gwamnan wanda ya je sakatariyar tare da wasu tsirarun mukarrabansa, bai samu ganawa da wani mamba na kwamitin ayyuka na kasa, NWC ba.

Sai dai ya dage cewa dole ne jam’iyyar ta bi ka’idojinta ko kuma ta shirya fuskantar shari’a, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Abin da Shaibu ya ce a ofishin shugaban PDP

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan barin ofishin mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Shaibu ya ce:

Kara karanta wannan

APC da dan takararta sun rufe karar da suke na kalubalantar zaben gwamnan PDP, bayanai sun fito

“Na zo ne don karbar takardar shaidar cin zabe saboda ni ne na ci zaben firamare a Edo bayan da wakilan zaben na gaskiya suka kada kuri’a.
“Yau ne aka ware don gabatar da takardar shaidar cin zaben kamar yadda jam’iyyar ta ce, don haka dole ne PDP ta bi ka’idojinta."

Shaibu ya lashe zaben fidda gwani?

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa Philip Shaibu ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP bayan da wani tsagi na wakilan zaben suka ƙada masa kuri'arsu.

Yayin da jam'iyyar ta yi nata zaben a filin wasanni na Samuel Ogbemudia, an ruwaito cewa wakilan da suka zabi Shaibu sun yi nasu zaben ne a harabar gidansa da ke Edo.

Rikici dai ya mamaye jam'iyyar bayan da Shaibu ya zargi gwamnan jihar kan cewa shi ne ke kulla masa makarkashiya don kar ya samu tikitin takarar gwamnan Edo na jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel