Kebbi: Hukumar Zaɓe Ta Sanar da Ranar Zaɓen Ƙananan Hukumomi 21

Kebbi: Hukumar Zaɓe Ta Sanar da Ranar Zaɓen Ƙananan Hukumomi 21

  • Hukumar zaɓe ta jihar Kebbi KESIEC ta sanar da cewa ta shirya za ta gudanar da zaɓen kananan hukumomi a ranar 31 ga watan Agusta, 2024
  • Shugaban hukumar KESIEC, Aliyu Muhammad Mera ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar mai ɗauke da sa hannunsa
  • Ya buƙaci masu ruwa da tsaki da sauran jama'a su bai wa hukumar goyon baya domin ta gudanar da sahihin zaɓen kananan humumomi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kebbi - Hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kebbi (KESIEC) ta bayyana ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomi 21 na jihar.

KESIEC ta bayyana cewa za a gudanar da zaɓen wanda ya kunshi zaɓen ciyamomi da kansiloli a faɗin ƙananan hukumomin jihar a watan Agusta, 2024.

Kara karanta wannan

Alhazan Kano sun samu gata, an fara ciyar da su abinci kyauta a Saudiyya

Taswirar jihar Kebbi.
Ranar 31 ga watan Agusta za a yi zaben kananan hukumomi a jihar Kebbi
Asali: Original

Shugaban hukumar zaɓen, Aliyu Muhammad Mera, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar mai ɗauke da sa hannunaa a Birnin Kebbi, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe za a yi zaben a Kebbi?

Sanarwar ta nuna cewa za a gudanar da zaben ne a ranar 31 ga watan Agustan 2024. Ƴan takara za su fafata kan kujerun shugabannin kananan hukumomi 21 da kansiloli 225 a fadin jihar.

Hukumar ta sanar da cewa za a iya samun fom din tsayawa takara, da duk wasu takardu da suka shafi zaben a Sakatariyar KESIEC da ke Birnin Kebbi.

Har ila yau, hukumar zaɓen ta buƙaci masu ruwa da tsaki da sauran ɗaukacin al'ummar jihar su ba ta goyon baya a lokacin wannan zaɓe.

A cewar KESIEC da goyon bayan al'umma da haɗin kansu ne kaɗai hukumar za ta yi nasarar gudanar da sahihin zaɓe wanda kowa zai amince da shi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rabawa ƴan gudun hijira tsabar kudi da kayan Abinci, ya mayar da su gidajensu

Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu ne ke jagorantar jihar Kebbi karƙashin inuwar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Alhazan Kano sun zama ƴan gata

A wani rahoton kuma Gwamnatin jihar Kano ta fara ciyar da alhazan jihar sau biyu a kowace rana a masaukinsu da ke ƙasar Saudiyya.

A wata sanarwa da kakakin mataimakin gwamna, Shu'aibu Ibrahim, ya fitar ya ce gwamnati ta tura kwararrun likitoci su kula da maniyyatan Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262