Sanatan Kebbi Ya Faɗi Gwamnan Arewa da Ke Biyan Sojoji N500m Duk Wata Saboda Tsaro

Sanatan Kebbi Ya Faɗi Gwamnan Arewa da Ke Biyan Sojoji N500m Duk Wata Saboda Tsaro

  • Sanatan jihar Kebbi ya bayyana yadda Gwamna Nasir Idris ke bai wa sojoji N500m duk wata domin magance matsalar ƴan bindiga
  • Garba Maidoki ya ce duk da wannan kuɗin da sojojin ke karɓa babu wani abin a zo a gani da suke yi don tsare rayukan mutanen Kebbi
  • Ya kara da cewa an gano wasu garuruwa a mazaɓarsa da ƴan bindiga suka matsa wa lamba kuma har yanzun sojoji ba su ɗauki mataki ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kebbi - Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi yana biyan sojoji kuɗi Naira Miliyan 500 duk wata domin su gudanar da ayyukan sa ido da sintiri.

Sanata mai wakiltar mazaɓar Kebbi ta Kudu, Garba Maidoki ne ya bayyana hakan a zaman majalisar dattawan Najeriya na ranar Talata.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya faɗi yadda suka shirya tsige sarakuna 5 da Ganduje ya naɗa a Kano

Gwamnan Kebbi, Nasir Idris.
Sanatan Kebbi ta Kudu ya ce sojoji na samun N500m duk wata daga Gwamna Idris Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Asali: Facebook

Sanata Maidoki, mamban jam'iyyar PDP ya faɗi haka ne yayin da yake ƙarin haske kan kudirin da Sanata Isah Jibrin (APC, Kogi ta Gabas) ya gabatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Premium Times ta tattaro, Sanata Isar Jibrin ya gabatar da kudiri domin sake raya kauyukan da ƴan bindiga suka lalata a ƙaramar hukumar Omala ta jihar Kogi.

Meyasa Gwamna Nasir ke biyan sojoji?

Da yake bayar da gudummuwa kan kudurin, Sanatan Kebbi ta Kudu, Maidoki ya ce:

"Gwamnan jiha ta ya faɗa mana cewa duk wata yana kashe wa rundunar sojoji N500m, ina kuɗin suka ɓata?"

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya tambayi Sanatan ko yana da shaidar da ke nuna cewa Sojojin Najeriya na karbar kudin kamar yadda ya yi ikirari.

Sanata Maidoki ya ba shi amsa da cewa kawai dai yana faɗin abin da Mai Girma Gwamna Idris ya faɗa masa ne.

Kara karanta wannan

NAHCON ta faɗi dalilin rashin fara jigilar alhazan Kano da wasu jihohi 6, ta gama da Nasarawa

"A zahiri dai abin da ya faɗa mana kenan, na ɗauko kalaman da gwamnan Kebbi ya furta ne kawai,"

- Sanata Garba Maidoki

Maidoki ya koka kan rashin tsaro

Sai dai ya gargadi sojoji da su daina dogara ga kudaden gwamnonin jihohi kadai kafin su haɗa tawagar sojoji domin yin aikinsu, The Cable ta ruwaito.

Maidoki ya ci gaba da cewa duk da kuɗin da sojoji ke karɓa duk wata, ƴan ta'adda sun mamaye kauyuka da dama kuma rayuwar mutane na cikin haɗari a Kebbi.

A cewarsa, akwai wasu kauyuka uku da ƴan bindiga ke yawan kai hare-hare a mazaɓarsa amma babu wani mataki da dakarun sojoji suka ɗauka duk da kuɗin da gwamna ke ba su.

Mutum 50 suka mutu a harin Wase

Rahotanni sun nuna cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a harin da ƴan bindiga suka kai yankin Wase ya karu zuwa 50

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya nuna damuwa da harin masallaci a Kano, ya aike da saƙo ga Gwamna Abba

Basaraken Wase, Alhaji Ahmed Lawal, ya ce an yi wa mamatan jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada a jihar Filato

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel