Gwamna Ya Rabawa Ƴan Gudun Hijira Tsabar Kudi da Kayan Abinci, Ya Mayar da Su Gidajensu

Gwamna Ya Rabawa Ƴan Gudun Hijira Tsabar Kudi da Kayan Abinci, Ya Mayar da Su Gidajensu

  • Gwamna Babagana Umaru Zulum ya fara kashin farko na shirin mayar da ƴan gudun hijira gidajensu a kananan hukumomi 9 na Borno
  • Ya kuma raba masu maƙudan kudi da suka kai N954.7m sannan kuma ya ba su kayayyakin abinci domin su sake gina rayuwarsu
  • A jawabinsa, Gwamna Zulum ya ce babu wanda aka yiwa dole, su da kansu suka nemi a mayar da su gida ko wurare masu tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya kaddamar da shirin mayar da ‘yan gudun hijira zuwa gidajensu a kananan hukumomi tara da ke jihar.

Bugu da ƙari, Gwamna Zulum ya rabawa waɗanda za a mayar gida N954.7m domin su farfaɗo da sana'o'insu kuma su samu abubuwan dogaro da kai.

Kara karanta wannan

Katsina: Ƴan bindiga sun kai hari, sun kashe gomman mutane a garuruwa 13

Babagana Zulum.
Gwaman Zulum ya maida yan gudun hijira gidajensu a kananan hukumomi 9 Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum
Asali: Twitter

Kimanin ƴan gudun hijira 12,985 da suka haɗa da magidanta maza 4,880 da mata 1,230, matan aure 6,875 da sauran ƴan uwa ne aka tsara za su koma gida a Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Gwamna Zulum ya tsara shirin

Jaridar Leadership ta tattaro cewa gwamnatin Borno ta tsara mayar da mutanen kauyukansu a kananan hukumomi shida a kashin farko.

Ƙananan hukumomin da za a fara da su sun ƙunshi Bama, Konduga, Gwoza, Kukawa, Jere da kuma Ngala, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kowane mutum ɗaya daga cikin magidanta maza 4,880 da mata 1,230 sun samu N100,000 yayin da matan aure 6,875 kuma aka raba masu N50,000 kowace ɗaya.

Zulum ya raba masu tallafin abinci

A jawabinsa Gwamna Zulum ya ce bayan rabon tallafin kudi, matan auren 6,875 sun kuma samu tallafin masara, shinkafa, katifa, mai da kayan abinci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu a faifayi: Ko ya cika manyan alkawuran da ya yi a cikin shekara 1?

Gwamnan ya kuma bayyana cewa kayayyakin abincin da aka rabawa ƴan gudun hijiran na daga cikin tallafin da gwamnatin tarayya ta turo ma jihar Borno.

"NEMA ta kawo mana waɗannan kayan abincin da muke rabawa mutanen da muka mayar gida. Kwanakin baya muka fara rabon kayan abincin da gwamnatin tarayya ta ba mu a Pulka."
"Babu wanda aka yi ma dole, dukkan ƴan gudun hijiran nan sun nemi a mayar da su gidajensu ko wasu wurare da aka samu zaman lafiya da kwanciyar hankali."

- Babagana Zulum.

Gwamnan Bauchi ya tsige kantoma

Kun ji labarin Gwamna Bala Mohammed Ƙauran Bauchi ya tsige shugaban ƙaramar hukumar Alkaleri, Hon Bala Ibrahim tare da mataimakinsa.

Sakataren gwamnatin Bauchi, Barista Ibrahim Kashim Mohammed ya sanar da haka a wata takarda da ya tura ma'aikatar ƙananan hukumomi da masarautu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262