Tsohon Akanta Janar da Shugaban Ƙaramar Hukuma Sun Fice Daga PDP Zuwa APC

Tsohon Akanta Janar da Shugaban Ƙaramar Hukuma Sun Fice Daga PDP Zuwa APC

  • Jam'iyyar PDP reshen jihar Abia ta ƙara rasa manyan jiga-jiganta yayin da ake shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027
  • Tsohon Akanta Janar, Gabriel C. Onyendilefu da tsohon shugaban ƙaramar hukuma sun bar PDP zuwa jam'iyyar APC
  • Wannan na zuwa ne makonni ƙalilan bayan tsohon kakakin majalisar dokokin Abia, Hon. Chinedum Orji, ya jagoranci magoya baya zuwa APC

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Tsohon Akanta Janar na jihar Abia, Gabriel C. Onyendilefu, ya sauya sheƙa daga Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar APC mai mulkin ƙasa.

Haka nan kuma tsohon shugaban ƙaramar hukumar Isiala Ngwa ta Kudu wanda bai jima da sauka b, Honorabul Ikechukwu Anyatonwu, ya bi sahunsa zuwa APC.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya tsige shugaban OORBDA, ya naɗa mutum 2 a manyan muƙamai

Tsohon Akanta Janar, Gabriel C. Onyendilefu.
Tsohon Akanta Janar da ciyaman sun koma jam'iyyar APC a Abia Hoto: The Ingenious
Asali: Facebook

Onyendilefu, tsohon ɗan takarar majalisar tarayya a mazaɓar Isiala Ngwa ta Arewa da ta Kudu a inuwar PDP, ya koma APC ne a mahaifarsa, Ikem Nvosi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Nation ta tattaro cewa Mista Onyendilefu ya riƙe muƙamin Akanta Janar a gwamnatin Teodore Orji da tsohon gwamna, Okezie Ikpeazu.

Meyasa jiga-jigan suka koma APC?

Da yake bayyana dalilinsa ya shiga APC, tsohon Akanta Janar ya ce:

"Babu wani zaɓi da ya wuce hakan ga mutumin da ke son a dama da shi a matakin siyasar ƙasa, kuma wannan mataki da na ɗauka shi ne ya fi dacewa a yanzu.
"A zahiri mun sha wahala sosai a siyasar yanki da jiha, lokaci ya yi da zamu matsa gaba."

Ana barin PDP zuwa APC a Abia

Wannan sauya sheƙa da tsohon Akanta Janar ya yi na zuwa ne makonni bayan wasu manyan jiga-jigan PDP sun tattara sun koma jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Ganduje: Shirin tsige shugaban APC na ƙasa da maye gurbinsa ya gamu da cikas

Daga cikin waɗanda suka sauya shekar har da tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Abia ta 7, Honorabul Chinedum Orji da wasu manyan ƴan siyasa, cewar Daily Post.

Legit Hausa ta fahimci cewa yawan ƙusoshin jam'iyyar PDP da ke barin jam'iyyar suna komawa APC ne maimakon jam'iyyar LP mai mulkin jihar Abia.

PDP ta naɗa kwamitin kamfen Edo

A wani rahoton kuma Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa zai jagoranci kwamitin PDP mai mambobi 152 na yakin neman zaben gwamnan Edo.

Sakataren yada labaran jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel