Gwamna Ya Maye Gurbin Kwamishinoni 8, Ya Tura Sunaye Ga Majalisar Dokoki
- Yayin da rikicin siyasar jihar Ribas ke ƙara tsananta, Gwamna Simi Fubara ya tura sunayen mutum 8 da za su maye gurbin mutanen Nyesom Wike
- Majalisar dokokin jihar mai goyon bayan Fubara ta ce za ta tantance sababbin kwamishinonin da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar yau Talata
- Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan bayan kwamishinonin da ke goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike sun ajiye aiki a gwamnatin Fubara
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - 'Yan majalisar dokokin jihar Ribas na tsagin Gwamna Siminalayi Fubara za su fara tantance sababbin kwamishinoni takwas da aka naɗa.
Ana tsammanin ƴan majalisar na iya tabbatar da naɗin kwamishinonin waɗanda za su maye gurbin mutanen Wike da suka yi murabus daga mukamansu.
Kamar yadda Leadership ta ruwaito, ƴan majalisar za suyi aikin tantance sunayen mutanen da gwamna ya aiko masu ne a yau Talata, 21 ga watan Mayu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sunayen waɗanda gwamna Fubara ya naɗa
Sunayen waɗanda Gwamna Fubara zai so ya naɗa a matsayin kwamishinonin sun haɗa da: Charles Bekee, Collins Onunwo, Solomon Eke da Dakta Peter Medee.
Sauran su ne Honorabul Elloka Tasie-Amadi, Honorabul Basoene Benibo, Tambari Sydney Gbara, da kuma Dakta Ovy Orluideye Chukwuma.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da magatakardar majalisar dokokin, Godsgift Gillis-West, ya fitar, PM News ta ruwaito.
Za a tantance kwamishinoni a majalisa
Sanarwar ta bukaci waɗanda aka zaba su hallara a zauren majalisar da ke gidan gwamnatin jihar Ribas a Fatakwal da misalin ƙarfe 10:00 na safe.
"Waɗanda aka naɗa su tabbata sun taho da kwafi 12 na takardar bayanan su (CV) da kuma takardun karatunsu na asali da kuma kwafi," in ji sanarwar.
Meyasa Fubara ya naɗa mutum 8?
Da alamu dai wadanda aka nada za su cike giɓin da wasu tsofaffin kwamishinonin da ke goyon bayan Ministan Abuja Nyesom Wike suka tafi suka bari.
Wannan na zuwa ne mako ɗaya bayan Gwamna Fubara ya rantsar da Dagogo Iboroma (SAN) a matsayin sabon Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na Ribas.
Jonathan ya sa baki a rikicin Rivers
A wani rahoton kuma Goodluck Jonathan ya nuna damuwa kan rikicin siyasar da ke faruwa tsakanin Nyesom Wike da magajinsa, Siminalayi Fubara.
Tsohon shugaban ƙasar ya buƙaci a kawo ƙarshen wannan rikici a Ribas yayin da alaƙa ke ƙara tsami tsakanin manyan jiga-jigan biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng