Wike v Fubara, Ganduje v Abba da Wasu Manyan Gwabzawa 6 da Ake Jira a 2027
Abuja - Idan abubuwa suka cigaba da tafiya a yadda suke a fagen siyasa, za a ga wasu manyan yaki a rumfunan kada kuri’a a 2027.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Rahoton nan ya yi hasashen manyan gwabzawar da za a iya cin karo da su a zaben 2027.
Rikicin da za a iya yi a 2027
1. Benue: Akume ko Alia a APC
A yanzu akwai mummunan rikicin gida a jam’iyyar APC a Benuwai, sabani ya shiga tsakanin gwamnan jihar da sakataren gwamnatin tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ba a ga maciji tsakanin Mai girma Hynthia Alia da Sanata George Akume wanda ya yi mulki a baya, rikicin nan zai iya yin kamari a zabe na gaba.
2. Zamfara: Dauda v Matawalle a 2027
Watakila abin da ya faru a 2023 ya maimaita kan shi nan da shekaru uku. Da yiwuwar Bello Matawalle ya sake tsayawa takarar gwamnan Zamfara.
Idan har ministan tsaron ya samu tikitin jam’iyyar APC, babu mamki ya gwabza da gwamna Dauda Lawal wanda ya doke shi, ya gaje kujerarsa a PDP.
3. Kano: Kwankwasiyya da Gandujiyya
Ana rade-radin Abba Kabir Yusuf zai iya sauya sheka daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, idan hakan ba ta faru ba, akwai kallo a Kano a zaben 2027.
Muddin alakar Abba Kabir Yusuf da Rabiu Kwankwaso ba ta canza ba, ana ganin zai fuskanci kalubale daga wanda Abdullahi Ganduje suka tsaida.
4. Wike da Fubara suna jiran zuwan 2027
Wani fadan kallo shi ne na yaran gwamna Simi Fubara da tsohon ubangidansa Nyesom Wike wanda tun suka raba gari tun kafin a dade a mulki.
Wike ya fara nadamar kawo Fubara a zaben 2023, alamu sun nuna gwamnan zai dage wajen ganin ya zarce a ofis, za a ga yadda za a buga a PDP.
5. Uba Sani da Malam El-Rufai
Masu hasashen siyasa suna ganin idan abubuwa ba su canza ba, baraka za ta iya shiga tsakanin gwamnatin Uba Sani da mutanen Nasir El-Rufai.
Kusan Malam El-Rufai ya yiwa Uba Sani riga da wando a Kaduna, amma kalaman da yake yi sun bude kofar samun rashin jituwa tsakaninsu a APC.
Rikicin siyasar Ribas kafin 2027
Rahoto ya zo cewa wani mutumin Nyesom Wike ya tabo gwamnan jihar Ribas, amma tuni Mai girma Simi Fubara ya maida martani.
Maganar da gwamnan Ribas ya yi tayi kaushi, ana tunanin wani tsohon kwamishinansa yake yiwa raddi, ya kira shi 'dan kwaya.
Asali: Legit.ng