"Daman Kwankwaso Bai Son Ganduje Tun a Tashin Farko", Farfesa a Kano Ya Magantu

"Daman Kwankwaso Bai Son Ganduje Tun a Tashin Farko", Farfesa a Kano Ya Magantu

  • Wani mai fashin baki a harkar siyasa a jihar Kano ya magantu kan alakar da ke tsakanin Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Ganduje
  • Farfesa Habu Mohammed ya ce tun farko daman Kwankwaso bai so zaben Ganduje a matsayin magajinsa ba kawai shugabannin jam'iyya suka yi sanadi
  • Farfesan ya ce alaka ta kara tsami ne bayan Ganduje ya hau mulki inda ya fara kaucewa tsare-tsaren Kwankwasiyya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Wani mai fashin bakin siyasa a jihar Kano, Farfesa Habu Mohammed ya yi tsokaci kan rikicin Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje.

Farfasa Habu wanda shi ne daraktan Cibiyar Dimukuraɗiyya a Jami'ar Bayero da ke Kano ya fadi ainihin silar rikicin.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Farfesa a Kano ya magantu kan rikicin Kwankwaso da Ganduje
Farfesa Habu Mohammed ya yi tsokaci kan rikicin Rabiu Kwankwaso da Abdullahi Ganduje. Hoto: @KwankwasoRM, @Imranmuhdz.
Asali: Twitter

Farkon rikicin Kwankwaso, Ganduje a Kano

Farfesan ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar Punch a karshen wannan mako da muke ciki a Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan ya ce rikicin ya fara ne lokacin da Kwankwaso zai kammala wa'adinsa na gwamnan da kuma neman magaji.

Ya ce asali ba shi ba ne zabinsa amma shugabannin jam'iyyar suka yi ruwa da tsaki domin ganin an tabbatar da Ganduje.

"Rikicin Kwankwaso da Ganduje ya fara ne tun da jimawa, mutanen biyu abokan juna ne wadanda suka yi aiki a ofisoshi a Abuja da kuma Kano a tare."
"Suna mutunta juna sosai kafin komai ya dagule lokacin da Kwankwaso ya fara shirye-shiryen barin ofis."
"Kwankwaso na kokarin neman wanda zai gaje shi saboda ba Ganduje ba ne zabinsa, sai da shugabannin jam'iyyar suka nuna goyon baya ga Ganduje kafin Kwankwaso ya amince ba a son ransa ba."

Kara karanta wannan

Ganduje ya cire tsoro, ya fadi musabbabin abin da ya jefa Arewa a matsala

- Farfesa Habu Mohammed

Ganduje ya nemi 'yanci gun Kwankwaso

Habu ya ce alakar ta kara dagulewa bayan Ganduje ya dare kujerar mulki a Kano lokacin da ya nuna yana son zama mai gashin kansa.

Ya ce Ganduje tun farkon hawa mulki yana tare da Kwankwasiyya da tsare-tsarensu amma daga baya ya nuna ya gaji tare da cire jar hula.

APC ta magantu kan matsalar Ganduje

Kun ji cewa jam'iyyar APC ta yi martani kan yadda Bola Tinubu bai tsoma baki kan matsalar da shafi Abdullahi Ganduje ba.

Jam'iyyar ta ce Tinubu ya damu APC amma saboda ayyukan da ya saka a gaba sun yi masa yawa ba komai ya ke martani a kai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel