Katsina: Manyan Dalilai 3 da Suka Tilastawa Shema Watsar da PDP Zuwa APC

Katsina: Manyan Dalilai 3 da Suka Tilastawa Shema Watsar da PDP Zuwa APC

Jihar Katsina - A makon da ya gabata tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema ya sauya sheka daga PDP zuwa jami'iyyar APC mai mulkin jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Komawar Shema APC bai zo da mamaki ba ganin yadda ya taka rawa wurin goyon bayan jam'iyyar APC musamman a zaben gwamnan jihar.

Dalilai 3 da suka saka Shema barin PDP zuwa APC a Katsina
Tsohon gwamnan Katsina, Shehu Shema ya watsar da PDP ne zuwa APC Kan wasu dalilai. Hoto: @MSIngawa.
Asali: Twitter

Shema ya ba Atiku shawara kan zabe

Bayan sanar da Bola Tinubu wanda ya lashe zabe, Shema ya shawarci Atiku Abubakar ya karbi sakamakon zaben da hannu bibbiyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani PDP ta dakatar da shi kan zargin zagon kasa inda daga baya ta janye matakin bayan ya yi barazanar fita daga jam'iyyar, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

An zargi wani jami'in KEDCO da kashe abokinsa saboda abin duniya

Legit Hausa ta jero muku manyan dalilai da ya sanya Shema komawa APC daga PDP.

1. Rasa ikon Shema a tafiyar PDP

Hadimin Shema a bangaren yada labarai, Olawale Oluwabusola ya zargi cewa an kaskantar da tsohon gwamnan a jam'iyyar wanda ya saka shi juya mata baya.

Babban matsalar da Shema ya fara samu a jam'iyyar a 2019 ne bayan Yakubu Lado ya yi nasara kan wanda ya tsayar a zaben fidda gwani.

Duk da haka Shema ya samar da mataimaki a zaben inda ya kawo Salisu Majigiri ga Yakubu Lado wanda suka yi rashin nasara bayan Aminu Masari na APC ya lashe zabe.

A 2023, Lado ya sake samun nasara a zaben fidda gwani inda ya ƙi daukar na hannun daman Shema wanda hakan ya saka tsohon gwamnan da mukarrabansa suka janye goyon bayansu ga Lado.

2. Shigowar Mustapha Inuwa PDP

Wani babban matsala da Shema ya samu bai rasa nasaba da shigowar Mustapha Inuwa PDP bayan ya rasa tikiti a APC.

Kara karanta wannan

"An yi watsi da su": Jigon APC ya magantu kan halin da El-Rufai da Yahaya Bello ke ciki

Inuwa wanda tsohon sakataren gwamnatin jihar ne ya kasance ba ya ga maciji da Shema tun suna gwamnatin marigayi Umaru Yar'adua.

Tsawon shekaru takwas da Shema ya yi a kan mulki, Inuwa ya ci gaba da caccakar manufofinsa da tsare-tsarensa.

3. Shema da tafiyar Atiku a PDP

Watakila wni babban dalilin tsohon gwamnan shi ne yadda dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya yi masa.

Wasu daga cikin hadimansa sun bayyana cewa an mayar da Shema saniyar ware daf da zaben 2023 duk da tasirinsa a siyasar jihar.

Ana ganin barin Shema PDP zai kara lalata jam'iyyar saboda wasu jiga-jigai ka iya watsar da ita zuwa jam'iyyar APC.

Shema ya koma APC daga PDP

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema ya watsar da jam'iyyar PDP tare da komawa APC mai mulki.

Tun a watan Agustan 2023, Shema ya kai ziyara ga shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje a Abuja da ake zargin zai iya barin PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.