Yahaya Bello: Tsohon Shugaban APC Ya Dauki Zafi Kan Dambarwar, Ya Soki Gwamna Mai Ci

Yahaya Bello: Tsohon Shugaban APC Ya Dauki Zafi Kan Dambarwar, Ya Soki Gwamna Mai Ci

  • Yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan dambarwar Yahaya Bello, Adams Oshiomole ya fusata kan lamarin
  • Oshiomole ya ce abin takaici ne yadda tsohon gwamnan ya yi da kuma sulalewa da Gwamna Ododo ya yi da shi
  • Ya koka kan yadda ake tsoron fadan gaskiya kan manyan mutane masu mukami yayin da ake yayata talakawa idan suka sace akuya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban jami'yyar APC, Adams Oshiomole ya dauki zafi kan dambarwar Yahaya Bello.

Oshiomole ya nuna damuwa kan yadda gwamna mai ci zai saɓa doka domin kare mai gidansa.

Tsohon shugaban APC ya magantu kan dambarwar Yahaya Bello
Tsohon shugaban APC, Adams Oshiomole ya yi martani kan dambarwar Yahaya Bello. Hoto: Yahaya Bello, Adams Oshiomole.
Asali: Facebook

Wane martani Oshiomole ya yi kan Bello?

Kara karanta wannan

Kamar Kaduna, Gwamnan APC ya caccaki tsoffin gwamnoni, ya yi gargadi mai tsauri

Sanatan ya ce bai kamata a rinka jin tsoron fadan gaskiya ba ko da kuwa waye ne ya aikata laifi a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce kamar yadda ake bayyana talaka da ya saci akuya ya kamata ko waye ya aikata laifi a tuhume shi ba tare da tsoro ba.

Tsohon gwamnan jihar Edo ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da TVC News ta wallafa yayin wani taro a Abuja.

"A matsayina na tsohon gwamna, na san wasu tsoffin gwamnoni da suka ce basu da kudi domin biyan tallafi ga yaran talakawa game da iliminsu duk da suna tura 'ya'yansu ƙasashen ketare."
"Abin da bai kamata muna yi ba, idan ka yi zargi baka kira suna ba sai dukkanku ku zama abin zargi."
"Ta yaya tsohon gwamna da ya rasa kariya zai saɓa doka kuma gwamna mai ci ya sake saɓa doka domin ganin ya kare shi, wannan manyan matsalolin da muke fama da su kenan."

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya amince da karin mafi karancin albashi a N70,000? an gano gaskiya

- Adams Oshiomole

Oshiomole ya magantu kan addini

Oshiomole ya ce idan har za a rinka yayata ɗan talaka da ya saci akuya meyasa ake tsoron kiran sunayen manyan mutane da ke saba dokokin kasa.

Sanatan ya kara da cewa wata babbar matsala da ke damun al'umma ita ce addini, wasu na cewa idan ka yi imani da Yesu Almasihu zai yaye maka talauci, ya ce wannan karya ce.

Kotu ta ba shugaban EFCC sabon umarni

Kun ji cewa wata kotu da ke zamanta a jihar Kogi ya umarci shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya gurfana a gabanta.

Kotun ta ba da wannan umarnin ne saboda zargin saɓa matakin da ta dauka kan binciken tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.