2027: Matasan Arewa Sun Gano Shirin Kawo Cikas Ga Tinubu da 'Yan Siyasa Ke Ƙullawa

2027: Matasan Arewa Sun Gano Shirin Kawo Cikas Ga Tinubu da 'Yan Siyasa Ke Ƙullawa

  • An gano yadda wasu 'yan siyasa ke kokarin kawo cikas ga gwamnatin Bola Tinubu game da zaben 2027 da ke tafe
  • Kungiyar matasa ta Arewa Consultative Forum ita ta bayyana haka inda ta yabawa shugaban kasa kan irin abubuwan more rayuwa da ya kawo
  • Shugaban kungiyar, Yerima Shettima ya ce Tinubu ya yi kokari wurin inganta Najeriya yayin da nada kwararru a gwamnatinsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Matasan kungiyar Arewa Consultative Forum (AYCF) ta nuna damuwa kan makircin wasu 'yan siyasa kan Shugaba Bola Tinubu.

Kungiyar ta ce akwai wasu 'yan siyasa a Arewa da ke neman lalata damar shugaban a zaben 2027 wurin shiga lamuran gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun bayyana dalilansu na zuwa Amurka taron zaman lafiya

Matasan Arewa sun kadu da shirin wasu 'yan siyasa kan gwamnatin Tinubu
Matasan Arewa sun nuna damuwa kan shirin 'yan siyasa game da gwamnatin Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Zargin matasan Arewa game da Tinubu

Shugaba kungiyar, Yerima Shettima shi ya yi wanan zargi inda ya ce gwamnatin Tinubu ta kawo ayyukan ci gaba a Najeriya, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima ya yabawa shugaban kan irin jajirtattun ministoci da sauran mukarraban da ya nada a gwamnatinsa.

Matasan sun zargi wasu daga cikin manyan 'yan siyasa a Arewa da neman dagula lamarin siyasar Tinubu a yankin, cewar Daily Post.

Daga cikin zargin da matasan suka yi har da neman hada gwamnatin Tinubu fada da al'umma domin cimma burinsu na siyasa.

Matasan Arewa sun yabawa mukarraban Tinubu

Har ila yau, Shettima ya yabawa daraktan hukumar DSS, Yusuf Bichi inda ya ce ya taimaka wurin dakile matsalolin tsaron kasar.

Ya ce Bichi ya ba da gudunmawa wurin tabbatar da zakulo bayanan sirri tare da kare Najeriya daga miyagu a ciki da wajen kasar.

Kara karanta wannan

Hukumar 'yan sanda ta yi karin haske kan rade radin kai hari a Abuja

Ya ce shugaban ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila ya taka muhimmiyar rawa wurin tabbatar da tsare-tsare gwamnatin sun ba da abin da ake nema.

Tinubu ya magantu kan wahalar da ake sha

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sha alwashin ci gaba da ɗaukar matakai da za su inganta rayuwar al'ummar Najeriya.

Tinubu ya ce bai damu da wahalar da 'yan kasar za su shiga na kankanin lokaci ba idan za a samu biyan buƙata.

Shugaban ya yabawa karfin guiwar 'yan kasar inda ya ce hakan ya ke kara masa kwarin guiwa kan daukar matakai masu tsauri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.