Kwanakin PDP Za Su Zo Karshe, Tsohon ɗan Majalisar Tarayya Ya Sake Ficewa
- Yayin da rikicin PDP ke kara ƙamari, tsohon mamban Majalisar Tarayya a jihar Ebonyi ya yi murabus daga jam'iyyar
- Hon. Sylvester Ogbaba wanda ya wakilci Abakaliki/Izzi ya sanar da yin murabus din ne a jiya Laraba 24 ga watan Afrilu
- Ya ce ya kasance a jam'iyyar tun shekarar 1998 inda ya ce ya dauki wannan mataki ne a karan kansa bayan nazari mai zurfi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ebonyi - Jam'iyyar PDP ta sake shiga mummunan yanayi bayan tsohon 'dan Majalisar Tarayya ya fice daga jam'iyyar.
Hon. Sylvester Ogbaba ya yi murabus daga jam'iyyar a jiya Laraba 24 ga watan Afrilu.
Yaushe Ogbaba ya sanar da barin PDP?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon ɗan Majalisar ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ogbaba ya wakilci mazabar Abakaliki/Izzi a Majalisar Tarayya a jihar Ebonyi daga shekarar 1999 zuwa 2003.
Tsohon dan majalisar ya ce ya tura takarda dauke da sanarwar murabus din zuwa shugabannin PDP a matakin jihar da karamar hukuma da gundumar Anmegu Enyigba a jihar.
Ogbaba ya kasance a PDP tun 1998
"Ina mai sanar da ku cewa a hukumance na yi murabus daga jam'iyyar PDP a wannan jihar."
"Na dauki wannan mataki ne bayan nazari mai zurfi inda fahimci yanzu lokaci ya yi da ya kamata na bar PDP."
"Na kasance a jam'iyyar PDP tun shekarar 1998 wanda na bayar da gudunmawa sosai wurin ganin jam'iyyar ta samu ci gaba."
"Wannan mataki da na dauka a karan kai na ne kuma ina godiya da dukkan goyon baya da kuma shugabanci nagari."
- Sylvester Ogbaba
Jiga-jigai 8 sun watsar da PDP a Imo
A wani labarin, kun ji cewa wasu jiga-jigan PDP takwas sun yi fatali da ita inda suka fice daga jam'iyyar a jihar Imo.
Hakan bai rasa nasaba da murabus din tsohon gwamnan jihar, Emeka Ihedioha a farkon wannan mako da muke ciki.
Ihedioha wanda tsohon mataimakin kakakin Majalisar Tarayya ne ya ce PDP ta gaza yin adawa mai karfi ga jam'iyyar APC mai mulki.
Asali: Legit.ng