Jam'iyyar PDP Ta Yi Rashin Babban Jigo, Tsohon Gwamna Ya Kama Gabansa
- Hon Emeka Ihedioha, tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party
- Ihedioha, wanda ya ce ya shiga PDP a 1998 ya ba da dalilin ficewarsa da gazawar jam’iyyar wajen magance matsalolinta na cikin gida
- Sai dai tsohon dan majalisar ya ce zai ci gaba da bayar da gudunmawa da za ta taimaka wajen ci gaban dimokuradiyya a Najeriya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Imo - Wani tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Honarabul Emeka Ihedioha, ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Ihedioha ya bayyana cewa PDP ta gaza warware matsalolinta na cikin gida ko aiwatar da dokokinta da kuma gaza yin sahihiyar adawa ga jam’iyyar APC.
PDP ta yi taron kwamitin NEC
Murabus din nasa na zuwa ne kwanaki kadan bayan da jam’iyyar PDP ta gudanar da taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC), jaridar Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron dai an yi shi ne da nufin daukar matakan ladabtarwa kan wadanda ake zargi da yi wa jam’iyyar zagon kasa a babban zaben 2023.
Sai dai Ihedioha, ya bayyana murabus din nasa ne a wata wasika da ya aikawa shugaban jam’iyyar PDP na gundumar sa ta Mbutu a karamar hukumar Aboh Mbaise a jihar Imo.
Ihedioha ya fadi dalilin barin PDP
Ihedioha ya aika kwafin wasikar ga shugaban kwamitin amintattu na PDP (BoT), mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, da kuma shugaban jam’iyyar PDP na jihar Imo.
Talabijin na TVCNews ya ruwaito tsohon dan majalisar ya ce jam’iyyar da ya shiga a shekarar 1998 a ‘yan kwanakin nan ta dauki hanyar da ta saba da akidarsa.
Mista Ihedioha ya ce duk da murabus din da ya yi, zai ci gaba da bayar da gudunmawa da za ta taimaka wajen ci gaban dimokuradiyya a Najeriya.
Matatar Dangote ta rage farashin dizal
A wani labarin na daban, Legit Hausa ta rahoto matatar Dangote ta sanar da sake zabtare farashin dizal da man jiragen sama domin saukakawa 'yan Najeriya.
Shugaban sashen sadarwa na rukunin Dangote, Anthony Chiejina ya ce farashin dizal yanzu ya koma N940 yayin da na jiragen sama ya koma N980.
Asali: Legit.ng