Biyu Babu: Bijirewa Shawarata ya Jawo Faduwar Peter Obi a 2023, Reno Omokri

Biyu Babu: Bijirewa Shawarata ya Jawo Faduwar Peter Obi a 2023, Reno Omokri

  • Reno Omokri, Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, ya ce ya shawarci Peter Obi ya hada kai da Atiku Abubakar a zaben da ya gabata
  • Ya bayyana haka ne ta cikin shirin Mic on Podcast, inda ya ce Peter ya bijirewa shawarwarinsa na hadewa da Atiku har ta kai ya fadi zaben
  • A cewar Reno, hatta a shekara 2019 shi ne ya tallatawa Atiku Abubakar Peter Obi, wanda ya ke ganin hadewarsu wuri guda zai taikamaka matuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos -Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya ce sai da ya shawarci Peter Obi Kan yadda zai yi nasara a zaben 2023, amma ya ki ji.

Kara karanta wannan

Murna yayin da Kashim ya fadi yadda naira za ta kasance karkashin Tinubu, ya kawo dalillai

Ya ce ya san idan Peter Obi ya tsaya takara, babu abin da za a cimma sai raba kuri'ar PDP.

Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan
Reno Omokri na ganin akwai nasara a hadewar Peter Obi da Atiku Abubakar. Hoto: Reno Omokri
Asali: Facebook

TheCable ta wallafa cewa Omokri na da yakinin hakan zai bawa Bola Ahmed Tinubu nasara maimakon Atiku ko Peter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

“Na fadawa Peter Obi cewa hanya mafi sauki da zai zama shugaban kasa shi ne ya tsaya takara a matsayin mataimakin Waziri Atiku Abubakar, kuma ya zama mai biyayya gare shi."

Tsohon mashawarcin shugaban kasar ya ce da Mista Peter Obi ya dauki shawarsa, Atiku na kammala wa'adin mulkin kasar nan, sai shi (Peter Obi).

Amma a yanzu, Omokri ya ce idan za a yi zabe sau 10, Peter Obi ba zai yi nasarar zama shugaban Najeriya ba.

"Na tallata Obi wajen Atiku Abubakar," Omokri

Reno Omokri ya kuma bugi kirjin cewa shi ne ya tallatawa Alhaji Atiku Abubakar ya dauki Peter Obi a matsayin mataimakinsa domin tsayawa takarar zaben 2019.

Kara karanta wannan

"Allah kaɗai ke ba da mulki," Atiku ya mayar da martani kan zargin cin amana a taron NEC

Omokri ya ce a wancan lokaci, Peter Obi ne ya fi cancantar zama dan takarar mataimakin shugaban kasar.

A wata hirar da ya yi ta shirin Mic on Podcast, ya kara da cewa sai da nemi shawarar Ubangidansa, Goodluck Jonathan kafin ya yanke shawarar tallata Obi ga Atiku, kamar yadda Vanguard News ta wallafa.

Bayan na tallata Obin ne Atiku ya amince ya dauke shi a matsayin mataimaki.

Reno Omokri ya ba da shawara kan Naira

A baya mun kawo muku yadda tsohon mashawarcin shugaban shugaban kasar, Reno Omokri su dinga sayen kayan da ake samarwa a cikin kasar nan domin farfado da darajar Naira.

Ya yabawa'yan Najeriyar dake kiraye-kirayen a sayi kayan da cikin gida, inda ya ce yin hakan zai taimaka wajen farfado da darajar Naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel