Murna Yayin da Kashim Ya Fadi Yadda Naira Za Ta Kasance Karkashin Tinubu, Ya Kawo Dalillai

Murna Yayin da Kashim Ya Fadi Yadda Naira Za Ta Kasance Karkashin Tinubu, Ya Kawo Dalillai

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana kwarin guiwarsa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya
  • Shettima ya ce ya na da tabbacin cewa darajar naira za ta ci gaba da tashi a kasuwanni kamar yadda ta ke yanzu
  • Wannan na kunshe ne a cikin sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a yau Asabar 20 ga watan Afrilu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa za a ci gaba da samun ci gaba a Najeriya.

Shettima ya ce bayyana kwarin guiwarsa kan yadda naira ke ci gaba da samun karuwar kan dala a mulkin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu ya dara shekaru 16 a PDP ta fuskar tsaro, Hadimin Tinubu

Kashim ya tabbatar da samun ci gaba a tattalin arziki karkashin Tinubu
Kashin Shettima ya yabawa Shugaba Tinubu kan ayyukan ci gaba a Najeriya. Hoto: @officialABAT, @KashimSM.
Asali: Twitter

Mene Shettima ke cewa kan Tinubu?

Ya ce ya na da tabbacin naira za ta ci gaba da samun daraja kan dala ganin yadda ta ke samun galaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin shugaban ya bayyana haka ne a yau Asabar 20 ga watan Afrilu a shafinsa na X.

"Naira ta shiga garari a baya, wasu suna murna, mu kuma muna musu dariya saboda mun san akwai shugabanci mai kyau."
"Tinubu ya san meye ya ke yi, tabbas naira ta na sake ta shi, kuma bambancin zai sake bayyana a gaba."

- Kashim Shettima

Ya yabi Tinubu kan cire tallafin mai

Yayin da ya ke magana kan cire tallafin man fetur, Kashim ya ce hakan ya zama dole domin dakile warwason kudi.

Ya ce an dauki matakin ne domin dakile wasu da ke zama hamshakan masu kudi a dare daya saboda karkatar da kudin tallafin da suke yi.

Kara karanta wannan

Ribadu ya fadi irin gatan da Tinubu ya yi wa Arewa fiye da yankinsa, ya kawo dalilai

Ya kara da cewa Shugaba Tinubu ya himmatu wurin dakile matsalolin kasar domin samar da ci gaba.

Har ila yau, Kashim ya bayyana yadda shugaban ya kawo ayyukan ci gaba a jihar Legas inda ya yaba masa kan kokarinsa a jihar.

Tinubu ya yi alkawari ga 'yan Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawari ga 'yan Najeriya kan halin kunci da ake ciki.

Shugaban ya bayyana cewa zuwa watan Disamba komai zai zama dai-dai a kasar duba da halin da ake ciki.

Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kasar ke cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa da ake ciki tun bayan cire tallafi..

Asali: Legit.ng

Online view pixel