Ganduje Ya Cika Baki, Ya Fadi Jihar APC da Jam'iyyun Adawa Ba Za Su Yi Nasara Ba

Ganduje Ya Cika Baki, Ya Fadi Jihar APC da Jam'iyyun Adawa Ba Za Su Yi Nasara Ba

  • Abdullahi Umar Ganduje shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya yi magana kan zaɓen jihar Ondo da yake tafe
  • Ganduje ya yi nuni da cewa jam'iyyar ce za ta yi nasara a zaɓen gwamnan jihar na watan Nuwamba mai zuwa
  • Ya bada tabbacin cewa jam'iyyar za ta gudanar da zaɓen fidda gwanin gwamna na gaskiya da adalci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gargaɗi jam'iyyun adawa kan jihar Ondo.

Ganduje ya shaida musu cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da riƙe madafun ikon jihar a zaɓen gwamna da za a yi a watan Nuwamba da ke tafe, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya bayyana babban abin da yake tsoro gabanin Zaɓen da jam'iyya ta shirya

Ganduje ya yi magana kan zaben Ondo
Ganduje ya hango nasara ga APC a zaben gwamnan Ondo Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Facebook

Ya yi wa ɗaukacin ƴan takara 16 na gwamnan Ondo na jam'iyyar APC alƙawarin samun daidaito a zaɓen fidda gwani da za a yi a ranar 20 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi magana ne ta bakin mataimakin sakataren tsare-tsaren jam'iyyar na ƙasa, Nze Chidi Duru a lokacin da yake karɓar fom ɗin nuna sha'awar tsayawa takara na Injiniya Ifeoluwa Oyedele, ɗaya daga cikin ƴan takarar gwamnan.

Me Ganduje ya ce kan zaɓen Ondo?

Gwamna Ganduje ya ce kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar ya duƙufa wajen ganin an bi ƙa’idojin da suka dace wajen gudanar da zaɓen fidda gwanin.

A kalamansa:

"Jam'iyyar tana da sha'awar gudanar da zaɓen fidda gwani na gaskiya da adalci a jihar Ondo.
"A wajenmu, shi ne tabbacin cewa bayan an kammala zaɓen, cikin ƴan takara 16 mutum ɗaya ne zai yi nasara, inda sauran za su taya duk wanda ya yi nasara murna kamar yadda muka yi a jihar Edo."

Kara karanta wannan

Jamiyyar APC ta bankado sabuwar makarkashiyar da gwamnan PDP yake kullawa

Da yake tuna yadda zaɓen fidda gwanin na jihar Edo ya kaya, shugaban jam'iyyar ta APC ya ce ƴan takara kaɗan da suka yi niyyar zuwa kotu, yanzu sun haƙura.

A kalamansa:

"Sun zo an yi sulhu, an tattauna kuma an zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya. Mun yi amanna cewa APC za ta lashe jihar Edo. Sannan idan mun yarda APC za ta yi nasara a jihar Edo, muna da cikakken ƙwarin gwiwa cewa APC za ta lashe jihar Ondo."

Ɗan Ganduje ya samu muƙami

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya ba Umar Abdullahi Ganduje babban mukami a hukumar samar da wuta a ƙauyuka (REA).

Tinubu ya nada Umar wanda ɗa ne ga shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje babban darektan ayyuka na hukumar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel