Rikicin PDP: Mummunar Zanga Zanga Ta Barke a Sakatariyar Jam'iyya, Bayanai Sun Fito

Rikicin PDP: Mummunar Zanga Zanga Ta Barke a Sakatariyar Jam'iyya, Bayanai Sun Fito

  • Zanga-zanga ta barke a sakatariyar jam'iyyar PDP yayin da wata kungiya ta bukaci dakatar da Nyesom Wike kan cin dunduniyar jami'yyar
  • Kungiyar PDP Reform Vanguard ta gudanar da zanga-zangar inda ta bukaci sauye-sauye a shugabancin jam'iyya na kasa
  • Wannan na zuwa ne bayan kusoshin jam'iyyar PDP sun tabbatar da ci gaba da kasancewar Damagun a matsayin shugaban jam'iyyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gungun matasa sun durfafi sakatariyar jami'yyar PDP a birnin Abuja yayin da ake tsaka da ganawa.

Wata kungiyar mai suna PDP Reform Vanguard ta mamaye sakatariyar inda ta bukaci a dakatar da Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Dino Melaye da tsohon gwamna sun gwabza kan Tinubu a taron PDP, an yaɗa bidiyon

Zanga-zanga ta barke a sakatariyar jami'yyar PDP da ke Abuja
Masu zanga-zanga sun bukaci a dakatar da Nyesom Wike daga PDP. Hoto: PRV.
Asali: UGC

Wasu bukatu kungiyar ta mika ga PDP?

Har ila yau, kungiyar ta bukaci shugaban jam'iyyar PDP, Umar Damagun da ya yi murabus daga mukaminsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasan sun dira a sakatariyar yayin da ake shirin gudanar da ganawar masu ruwa da tsakin jami'yyar, cewar rahoton Punch.

Sun zargi Ministan Abuja, Nyesom Wike kan cin amanar jam'iyyar PDP wanda ya cancanci a dakatar da shi.

Musabbabin zanga-zangar PDP a Abuja

Da yake magana kan dalilin zanga-zangar, Usman Seidu ya ce Damagun da Wike sun lalata jami'yyar PDP gaba daya.

Usman ya ce sun kuma kawo cikas a kokarin jami'yyar na kasancewa mai karfi a matsayin jam'iyyar adawa a Najeriya.

Ya yabawa tsohon shugaban PDP, Dakta Iyorchia Ayu kan irin jajircewa da ya yi tare da janye karar da ya shigar, cewar rahoton The Sun.

Kara karanta wannan

Kasar Yarbawa: Kotu ta rufe masu fafutukar raba Najeriya bisa zargin cin amana

Har ila yau, ya ce kasancewar Damagun sa Wike a cikin jam'iyyar babbar annoba ce da za ta nakasa jami'yyar duba da halin da ta ke ciki Yanzu.

PDP: Melaye ya yi arangama da Ortom

A baya, mun kawo muku labarin cewa Sanata Dino Melaye ya caccaki tsohon gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom kan goyon bayan Shugaba Bola Tinubu.

Dino Melaye ya samu matsala da tsohon gwamnan na Binuwai ne yayin ganawar shugabannin jam'iyyar PDP a Arewa ta Tsakiya.

An yi ganawar ne a jiya Laraba 17 ga watan Afrilu inda Melaye ya kalubalanci Ortom kan dalilin zuwansa wajen taron.

Asali: Legit.ng

Online view pixel