Benue: Tashin Hankali Yayin da Ƴan Sanda Suka Kwace Iko da Sakateriyar APC
- Jami'an rundunar ƴan sanda sun ƙara kwace iko da sakatariyar tsagin APC wanda Kwamared Austin Agede ke jagoranta a jihar Benue
- Rahoto ya nuna cewa tun da farar safiya, ƴan sanda suka girke motocin su, suka toshe duk wata hanya ta shiga sakateriyar a Makurɗi
- Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya haramta dukkan wasu tarukan siyasa da na jama'a a jihar saboda yanayin taɓarɓarewar tsaro
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - A karo na biyu cikin wata ɗaya tal, dakarun ƴan sanda na sashin yaƙi da masu tada tarzoma sun kwace iko da sakateriyar jam'iyyar APC da ke Makurdi a jihar Benuwai.
Ƴan sanda sun mamaye babbar sakatareyar All Progressive Congress (APC) wanda ke ƙarƙashin jagorancin Kwamared Austin Agade ranar Jumu'a.
Yadda APC ta dare biyu a Binuwai
The Nation ta tattaro cewa akwai sakatariya APC guda biyu a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai, ɗaya ta tsagin Agada yayin da ɗayar kuma tana ƙarƙashin Benjamin Omakolo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsagin Agada ya sanya ranar 19 ga watan Afrilu, 2024 watau yau Jumu'a domin rantsar da kwamitin tsare-tsaren zaɓen kananan hukumomin da ke tafe a jihar.
Meyasa ƴan sanda suka ɗauki matakin?
Amma tun da duku-duku, misalin ƙarfe 6:00 na safiyar Jumu'a, dakarum ƴan sanda suka girke motocinsu tare da toshe dukkan hanyoyin zuwa sakateriyar.
A halin yanzun da muke haɗa maku wannan rahoton, an shiga fargaba da tashin hankali kan wannan lamari.
An tattaro cewa ƴan acaɓa da ke goyon bayan tsagin APC karkashin Benjamin Omakolo da shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Benuwai sun ayyana cewa APC ta gaskiya ta karɓe ragama.
Idan ba ku manta ba a kwanakin baya Gwamna Hyacinth Alia ya haramta duk wasu harkokin da suka shafi tarukan siyasa da taron jama'a a jihar Benuwai.
Rahotanni sun tabbatar da cewa har yanzun umarnin Gwamna Alia na haramta duk wani nau'in taro yana aiki, cewar rahoton Within Nigeria.
Shugaban APC na cikin matsala
A wani rahoton wasu masu zanga-zanga sun mamaye hedkwatar APC ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja, sun nemi Abdullahi Ganduje ya yi murabus.
Mutanen sun buƙaci a soke duk wani mataki da Dr. Ganduje ya ɗauka bayan dakatar da shi kuma sun aike da saƙo ga shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng