Gwamnoni Sun Ɗauki Matsayi Kan Batun Sauya Shugaban PDP Na Ƙasa a Taron NEC

Gwamnoni Sun Ɗauki Matsayi Kan Batun Sauya Shugaban PDP Na Ƙasa a Taron NEC

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP sun musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ana shirin canja shugaban jam'iyya, Umar Damagum
  • Gwamna Bala Mohammed na Bauchi kuma shugaban kungiyar gwamnonin ya ce babu batun sauya shugabanci a ajendar taron
  • A yau Alhamis, 18 ga watan Afrilu ne kwamitin zartaswa na PDP ta ƙasa zai gudanar da taro a birnin tarayya Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babu wani shiri na sauya shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa a wurin taron kwamitin zartaswa ranar Alhamis, 18 ga watan Afrilu.

Gwamnonin jam'iyyar PDP karkashin jagorancin Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ne suka tabbatar da haka ga manema labarai jiya Laraba a Abuja.

Atiku da gwamnonin PDP.
Gwamnonin PDP sun musanta shirin sauya shugaban jam'iyya a taron NEC Hoto: OfficialPDPNig
Asali: Facebook

PDP: Gwamnoni na tare da Damagum

Kara karanta wannan

Dino Melaye ya caccaki tsohon gwamnan PDP da Wike da Atiku suka hadu, bidiyon ya yadu

A cewar ƙungiyar gwamnonin PDP, za su daƙile duk wani yunƙuri na kwace iko da jam'iyyar PDP daga ɗaiɗaikun mutane ko ƙungiyoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar gwamnonin ta ɗauki wannan matsaya ne a wurin taron da suka gudanar a masaukin gwamnan jihar Akwa Ibom da ke Abuja, The Nation ta ruwaito.

A cewar gwamnonin PDP, babu batun sauya shugabancin jam'iyyar a yanzu kamar yadda ake yaɗawa kuma sun shirya tunkarar ƙalubalen da PDP ke fuskanta.

Gwamnonin PDP da suka halarci taron

Bayan Gwamna Mohammed na Bauchi wanda ya karanta sakamakon zaman taron, sauran gwamnonin da suka halarci zaman sun haɗa da Umo Eno na Akwa Ibom da Ahmadu Fintiri na Adamawa.

Sauran su ne, mataimakin shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, Siminalayi Fubara na jihar Ribas, Douye Diri na Bayelsa da Sheriff Oborevwori na jihar Delta.

Kara karanta wannan

Dakatar da Ganduje: Daga karshe an bayyana wadanda suka 'kitsa' shirin

Har ila yau, mataimakan gwamnan da suka halarci wurin taron sun haɗa da Omobayo Godwins (Edo) da Ifeanyi Ossai (Enugu), inji rahoton Independent.

PDP na shirin sauya shugabanta?

Gwamna Mohammed ya jaddada cewa babu batun canja shugabancin PDP a cikin a shirin taron NEC, kana ya ƙara da cewa jam’iyyar ba za ta iya karya kundin tsarin mulkinta ba.

"Mun shirya yin komai bisa tanadin kundin tsarin mulkin jam'iyyar PDP, saboda ba mu zo nan domin tattauna batun canja shugabancin jam'iyya ba.
"Muna kan batun yadda zamu warware matsalolon mu ne da kawo ci gaba ta yadda a ƙarshe idan lokaci ya yi za a gudanar da tarukan zaɓen sababbin shugabanni."

- Gwamna Mohammed, shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP.

Ganduje: APC ta mayar da martani

A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta ƙasa ta yi fatali da hukuncin babbar kotun jihar Kano kan dakatar da shugabanta na ƙasa, Abdullahi Ganduje

Mai ba APC shawara kan harkokin shari'a, Farfesa Abdulkarim Kana, ya ce za su kai ƙorafi ga NJC domin a tsawatarwa alkalin da ya ba da umarnin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel