Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye Hedkwatar APC, Sun Bukaci Ganduje Ya Yi Murabus

Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye Hedkwatar APC, Sun Bukaci Ganduje Ya Yi Murabus

  • Masu zanga-zanga sun kutsa kai babbar hedkwatar APC da ke Abuja kan batun dakatar da shugaban jam'iyya na ƙasa, Abdullahi Ganduje
  • Sun buƙaci a soke duk wani mataki da Dr. Ganduje ya ɗauka bayan dakatar da shi kuma sun aike da saƙo ga shugaban ƙasa Tinubu
  • A cewarsu, zaman Ganduje a wannan kujera barazana ce babba ga zaɓen fitar da ɗan takarar da za a yi a Ondo ranar Asabar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ga dukkan alamu tsugune ba ta ƙare ba a jam'iyyar APC kan batun dakatar da shugaban jam'iyya na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje.

A jiya Alhamis, 18 ga watan Afrilu, wasu masu zanga-zanga suka mamaye hedkwatar APC ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja, sun nemi Abdullahi Ganduje ya matsa gefe.

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Kotu ta bada umurni dabam kan dakatar da Ganduje

Shugaban APC na kasa, Ganduje.
Zanga-zangar Ganduje ta ɓarke a hedkwatar APC a Abuja ranar Alhamis Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Kamar yadda Daily Trust ta kawo, masu zanga-zangar sun buƙaci a soke duk wani mataki da shugaban jam'iyyar ya ɗauka, sannan ya yi murabus.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dandazon mambobin na APC sun ɗaga kwalaye da bana masu ɗauke da rubutu daban-daban, daga ciki sun ɓukaci Dakta Ganduje ya haƙura da shugabancin APC.

Ganduje da APC: An aika saƙo ga Tinubu

A wani sakon ƙorafi da suka aika zuwa ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, masu zanga-zangar sun ce ci gaba da zaman Ganduje a ofis barazana ce ga zaɓen fitar gwanin Ondo.

Ƙorafin da suka rubuta da nufin ya isa ga shugaban ƙasa ya samu sa hannun jagororin masu zanga-zangar, Denesi Momoh, Abdulkadir Shu'aibu da Adeyeye Olugbenga.

"Ran ka ya dade, yana da kyau mu ceci babbar jam’iyyarmu daga faɗawa matsala, ta hanyar tabbatar da soke duk wani mataki da aka dauka tun bayan dakatar da shugaban jam'iyya na ƙasa.

Kara karanta wannan

Dakatar da Ganduje: Daga karshe an bayyana wadanda suka 'kitsa' shirin

"Sannan duk wanda aka naɗa muƙaddashin shugaban jam'iyya a ba shi dama ya yi aiki saboda ka da zaben fitar da ɗan takara a jihar Ondo ya samu matsala," in ji su.

Ina mokomar Ganduje a jam'iyyar APC?

Wannan na zuwa ne bayan wasu matasa sun yi zanga-zangar nuna goyon bayansu ga shugabancin Ganduje, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Idan ba ku manta ba mai ba APC shawara kan harkokin shari'a, Abdulkarim Kana, ya ce umarnin kotu na dakatar da Ganduje ba zai yi aiki ba saboda ta hanyar damfara aka samo shi.

APC ta magantu kan umarnin kotu

A wani rahoton kuma jam'iyyar APC mai mulki ta ce ta samu labarin umarnin kotu na dakatar da shugabanta na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje

Mai ba jam'iyyar shawara kan harkokin shari'a, Abdulkarim Kana, ya ce amma har yanzun umarnin bai zo hannun APC ba tukuna a rubuce.

Asali: Legit.ng

Online view pixel