Ganduje Na Nan a Matsayin Shugaban APC Na Kasa Bayan Hukuncin Kotu? Bayanai Sun Fito

Ganduje Na Nan a Matsayin Shugaban APC Na Kasa Bayan Hukuncin Kotu? Bayanai Sun Fito

  • Jam'iyyar APC ta jaddada cewa Dakta Abdullahi Umar Ganduje na nan daram a matsayinsa na shugaban jam'iyyar na ƙasa
  • Mai magana da yawun APC, Felix Morka, ya ce ba za su yi aiki da umarnin kotun farko ba, amma suna tare da hukuncin babbar kotun tarayya
  • Morka ya bayyana cewa a yanzu komai ya koma asalin yadda yake gabanin dakatar da Ganduje a gundumarsa da ke Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta ƙasa ta ce ba za tayi amfani da umarnin babbar kotun Kano na farko ba wadda ta tabbatar da dakatar da Abdullahi Ganduje.

Mai magana da yawun APC na ƙasa, Felix Morka, ya jaddada cewa jam'iyyar ba za ta kalli umarnin kotun farko na dakatar da Ganduje daga matsayin shugaban APC ba.

Kara karanta wannan

Mulkin Tinubu ya dara shekaru 16 a PDP ta fuskar tsaro, Hadimin Tinubu

Shugaban APC, Abdullahi Ganduje.
Ganduje zama daram a kujerar shugaban APC, in ji Felix Morka Hoto: OfficialAPCNig
Asali: Twitter

Jam'iyyar APC Ganduje ta sani a NWC

Jami'in ya kuma nanata cewa har yanzun ba a kawowa shugaban jam'iyya mai mulki takardar umarnin kotun ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Morka ya yi wannan furucin ne yayin da ya baƙunci wani shirin gidan talabijin na Arise a makon nan.

Maimakon haka, kakakin APC ya tabbatar da cewa suna goyon bayan hukuncin babbar kotun tarayya mai zama a Kano, wanda ta jingine dakatar da Ganduje.

Kotu ta bada sabon umarni a APC

Rikicin siyasar Kano ya ɗauki sabon salo bayan babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta tabbatar da Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar APC ranar Laraba.

Kotun dai ta ɗauki wannan matakin ne bayan tsohon gwamnan Kano ya shigar ƙarar neman a bi masa haƙƙinsa na saurarom ɓangarensa, cewar Punch.

Da yake mayar da martani, Morka ya ce wannan shi ke abin da ya dace saboda duk wannan kace-nace da ake ta yi waɗanda suka dakatar da Ganduje ba ƴaƴan APC ba ne.

Kara karanta wannan

'Babu wanda zai shigo APC sai da izinin Ganduje,' An ja kunnen Kwankwasiyya

Kakakin APC ya ce:

"Bai kamata kotun farko ta ba da wannan umarni ba saboda wasu dalilai. Na farko waɗanda suka shigar da ƙarar ba mambobin APC ba ne ba su da hurumi."

Wanene sahihin shugaban APC?

Mai magana da yawun APC ya ƙara da cewa bayan hukuncin babbar kotun tarayya, a yanzu komai ya koma asalin yadda yake gabanin lamarin dakatarwan nan ta ɓullo.

"A halin yanzun mun koma asalin yadda muke gabanin dakatar da Ganduje, yana nan daram a matsayin shugaban jam'iyya mai mulki ta ƙasa."

Ganduje ya ƙara shiga matsala a APC

A wani rahoton kuma masu zanga-zanga sun kutsa kai babbar hedkwatar APC da ke Abuja kan batun dakatar da shugaban jam'iyya na ƙasa, Abdullahi Ganduje.

Sun buƙaci a soke duk wani mataki da Dr. Ganduje ya ɗauka bayan dakatar da shi kuma sun aike da saƙo ga shugaban ƙasa Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel