Babbar Kotu Ya Yanke Hukunci Kan Yunkurin EFCC Na Cafke Tsohon Gwamnan Kogi

Babbar Kotu Ya Yanke Hukunci Kan Yunkurin EFCC Na Cafke Tsohon Gwamnan Kogi

  • Kotu ta hana hukumar yaƙi da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta kama, tsarewa da gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello
  • Alƙalin kotun mai shari'a I. A Jamil ya tabbatar wa da tsohon gwamnan haƙƙinsa na zama ɗan adam, ya ce bai halatta a tauye masa haƙƙi ba
  • Tun farko, Yahaya Bello ya buƙaci kotun ta masa iyaka da EFCC wacce ke neman kama shi ta gurfanar bisa zalunci a cewarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi - Babbar kotun jiha mai zama a Lokoja ta haramtawa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC kamawa, tsarewa da gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, mai shari'a I.A Jamil ne ya yanke wannan hukuncin a kara mai lamba HCL/68/M/2020 ranar Laraba, 17 ga watan Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

"Ɗaurin shekaru 5": EFCC ta ja kunnen gwamnan APC da masu kawo cikas kan Yahaya Bello

Yahaya Bello.
Kotu ta hana EFCC kama tsohon gwamnan jihar Kogi., Yahaya Bello Hoto: Yahaya Bello
Asali: Facebook

Alƙalin ya bayyana cewa bai halatta a tauye haƙƙin tsohon gwamnan ba, sai dai idan kotu ce ta ba da izini na daban, cewar rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dogaro da wannan umarni, an hana EFCC ta kama, tsarewa da gurfanar da wanda ya shigar da ƙara sai dai idan kotu ce ta ba da izini."

Ƙorafin da Yahaya Bello ya shigar kotu

Yahaya Bello dai ya shigar da kara ne a gaban babbar kotun jihar kan zargin EFCC da ƙoƙarin take masa hakkinsa na dan adam.

Tsohon gwamnan ya roƙi kotun ta ba da umarnin hana hukumar EFCC kama shi da tsare shi da kuma gurfanar da shi bisa zalunci.

Saboda haka, Kotu ta hana wadanda ake kara (EFCC) gurfanar da wanda ga shigar da ƙara har sai idan tana da kwararan hujjoji kan tuhumar da take masa.

Kara karanta wannan

Badakalar N84bn: Kotu ta amince da bukatar hukumar EFCC na cafke Yahaya Bello

Yahaya Bello: EFCC ta yi rashin nasara

Dangane da batun hurumin kotun na sauraron shari'ar, alkalin ya kori ƙorafin EFCC kana ya tabbatar da cewa kotun jihar tana da cikakken hurumi.

"Wannan kotun tana da cikakken hurumin sauraron wannan ƙara, saboda haka wanda yake ƙara ya samu nasara a batun kare haƙƙin ɗan adam," in ji alkalin.

Gwamnan Kogi ya ziyarci Bello a Abuja

Rahoto ya zo cewa Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi ya kai ziyara gidan Yahaya Bello a Abuja bayan jami'an EFCC sun mamaye gidan ranar Laraba

Ododo, wanda ya gaji Yahaya Bello ya isa gidan da ke Wuse 4 tare da dandazon matasa, waɗanda suka nuna takaicinsu da matakin EFCC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel