Gwamna Ododo Ya Ziyarci Gidan Yahaya Bello a Abuja Kan Abin da Jami'an EFCC Suka Yi

Gwamna Ododo Ya Ziyarci Gidan Yahaya Bello a Abuja Kan Abin da Jami'an EFCC Suka Yi

  • Gwamna Ahmad Usman Ododo na jihar Kogi ya kai ziyara gidan Yahaya Bello a Abuja bayan jami'an EFCC sun mamaye gidan ranar Laraba
  • Ododo, wanda ya gaji Yahaya Bello ya isa gidan da ke Wuse 4 tare da dandazon matasa, waɗanda suka nuna takaicinsu akn matakin EFCC
  • Ana zargin jami'an EFCC sun je ne da nufin kama Alhaji Yahaya Bello domin su gurfanar da shi a gaban ƙuliya kan badakalar maƙudan kuɗi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi ya ziyarci magabacinsa, Yahaya Bello, a gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja ranar Laraba.

Wannan na zuwa ne yayin da jami'an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) suka kai samame gidan Yahaya Bello.

Kara karanta wannan

Badakalar N84bn: Kotu ta amince da bukatar hukumar EFCC na cafke Yahaya Bello

Gwamna Ododo da Yahaya Bello.
Gwamna Ododo ya isa gidan Yahaya Bello na Abuja Hoto: Yahaya Bello
Asali: Facebook

Gwamna Ododo ya isa gidan Yahaya Bello na Abuja da ke layin Benghazi a Wuse Zone 4 da misalin ƙarfe 2:45 na rana yau Litinin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ododo ya samu rakiyar jami’an tsaro da magoya baya matasa da dama, waɗanda suka nuna takaicinsa da mamayar da EFCC ta kai gidan tsohon gwamnan.

Yadda EFCC ta mamaye gidan Bello

Tun da farko dai an ga tulin jami’an hukumar EFCC sun mamaye titin da gidan tsohon gwamnan jihar Kogi yake a Abuja.

A rahoton jaridar The Nation, jami'an hukumar yaƙi da rashawar sun taƙaita yanayin zirga-zirga a cikin da wajen titin gidan Yahaya Bello.

Har kawo yanzu babu wata sanarwa a hukumance da ta bayyana maƙasudin girke jami'an hukumar a wannan titi.

Bello: Meyasa EFCC ta ɗauki matakin?

Kara karanta wannan

EFCC: An yi ta harbe-harbe yayin da Gwamnan Kogi ya sulale da Yahaya Bello

Amma wata majiya daga cikin hukumar EFCC da ta yi magana da kwarin guiwa ta ce jami'an sun kadddamar da samame ne da nufin cafke tsohon gwamnan.

Da aka kara tambayarsa dalilin da ya sa jami’an suke son kama tsohon gwamnan, wani jami’i da ya nemi a sakaya sunansa, bai ƙara cewa komai ba.

An gano cewa lamarin ba zai rasa nasaba da badakalar Naira biliyan 84 da ake zargin Yahaya ba wanda hukumar EFCC ke ƙoƙarin gurfanar da shi a gaban kuliya.

APC ta soki hukuncin kotun Kano

A wani rahoton jam'iyyar APC ta ƙasa ta yi fatali da hukuncin babbar kotun jihar Kano kan dakatar da shugabanta na ƙasa, Abdullahi Ganduje.

Mai ba APC shawara kan harkokin shari'a, Farfesa Abdulkarim Kana, ya ce za su kai ƙorafi ga NJC domin a tsawatarwa alkalin da ya ba da umarnin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel