Atiku Ya Gamu da Cikas Yayin da Masu Zanga-Zanga Suka Mamaye Hedkwatar PDP a Abuja

Atiku Ya Gamu da Cikas Yayin da Masu Zanga-Zanga Suka Mamaye Hedkwatar PDP a Abuja

  • Mambobin PDP sun ɓarke da zanga-zanga, sun mamaye babbar hedkwatar jam'iyya ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja
  • Masu zanga-zangar sun jaddada goyon bayansu ga muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum da ministan Abuja, Nyesom Wike
  • Wannan na zuwa ne yayin da babbar jam'iyyar adawa ta shirya taron majalisar zartaswa (NEC) domin yanke makomar shugaban jam'iyyar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Wasu gungun masu zanga-zanga sun mamaye babbar hedkwatar Peoples Democratic Party (PDP) da ke birnin tarayya Abuja.

Masu zanga-zangar sun ayyana cikakken goyon bayansu ga muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum da ministan birnin tarayya, Nyesom Wike.

Damagum da Wike.
Damagum da Wike sun samu karin goyon baya gabanin taron NEC Hoto: Umar Damagum, Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, masu zanga-zangar sun ɗaga allunan sanarwa masu ɗauke da rubutun da ke nuna goyon bayansu ga Wike da Damagum.

Kara karanta wannan

Dakatar da Ganduje: Daga karshe an bayyana wadanda suka 'kitsa' shirin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana cewa suna zargin wasu tsirarin mutane a cikin jam'iyyar PDP na ƙoƙarin haifar da rashin jituwa da rabuwar kawuna a tsakanin shugabannin jam'iyya.

Abubuwan da ke faruwa a PDP

Zanga-zangar dai na faruwa ne sa’a guda kafin taron gwamnonin jam’iyyar PDP, kuma sa’o’i 24 gabanin taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP ta kasa (NEC).

Ana sa ran za a tattauna batun shugabancin babbar jam'iyyar adawar a taron NEC wanda zai gudana ranar Alhamis, 18 ga watan Afrilu, 2024.

A baya-bayan nan dai PDP ta fuskanci hargitsi daga wasu ‘ya’yanta, inda suka yi kira ga kwamitin ayyuka na kasa (NWC) karkashin Damagum ya yi murabus.

Fusatattun mambobin sun buƙaci Damagum da sauran mambobin NWC su yi murabus ne saboda gazawarsu wajen tafiyar da jama'iyyar PDP yadda ya dace.

Kara karanta wannan

Dakatar da Ganduje: Jam'iyyar APC ta mayar da martani kan hukuncin babbar kotun Kano

Wannan ci gaban na zuwa ne bayan NWC, a wata sanarwa da sakataren yada labarai, Debo Ologunagba, ya fitar a X, aka kaɗa kuri'ar amincewa da shugabancin Umar Damagum.

Shugabanni zasu gana da Ganduje

A wani rahoton Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jamiyyar APC na ƙasa zai samu baƙi a sakatariyar jam'iyyar ta ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Shugabannin jam'iyyar na mazaɓun da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa za su ziyarci Ganduje domin nuna goyon bayansu a gare shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel