Tsoffin Gwamnoni 4 da Sanatocin Arewa 8 a Majalisa da Ba Su Gabatar da Kudiri Ba a Watanni 10
FCT, Abuja - Tun bayan kaddamar da Majalisar Dattawa ta 10 a watan Yunin 2023, akwai Sanatoci da ba su kawo ko da kudiri guda daya ba.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
A binciken da Daily Trust ta yi, ta gano cewa akwai tsoffin gwamnoni hudu da Sanatoci 21 da suke ɗumama benci tsawon wannan lokaci.
Akalla akwai tsoffin gwamnonin 13 a Majalisar wanda hudu daga cikinsu ba su yi wani katabus ba tun bayan shigowarsu Majalisar.
Tsoffin gwamnoni marasa kudiri a majalisa
Legit Hausa ta jero muku tsoffin gwamnonin da kuma wasu sanatoci da ba su yi abin a zo a gani ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Abdul'aziz Yari - Zamfara ta Yamma (APC)
Sanata Abdul'aziz Yari shi ne tsohon gwamnan jihar Zamfara wanda ya nemi shugabancin Majalisar a bara.
Yari na daga cikin tsoffin gwamnonin da ba su kawo wani kudiri da zai taimakawa al'umma ba, cewar rahoton The Citizen.
2. Adams Oshiomole - Edo ta Arewa (APC)
Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole ya daɗe a Majalisar tun bayan barin kujerar shugabancin jam'iyyar APC a Najeriya.
Sai dai sanatan ya tabbatar da cewa ya gama shirya kudirinsa kuma zai gabatar da shi nan ba da jimawa ba.
3. Seriake Dickson - Bayelsa ta Yamma (PDP)
Tsohon gwamnan jihar Bayelsa ya sha rantsuwa a Majalisar ne a watan Yunin shekarar 2023 bayan kammala wa'adinsa na mulkin jihar.
Sanatan na daga cikin tsoffin gwamnonin da suka gaza gabatar da wani kudiri a Majalisar tun bayan kaddamar da ita.
4. Simon Lalong - Filato ta Kudu (APC)
Simon Lalong bai samu zarafin gabatar da wani kudiri ba a Majalisar duk da shafe akalla watanni hudu.
An rantsar da Lalong ne a Majalisar a watan Disambar 2023 bayan samun nasara a Kotun Daukaka Kara.
Sauran sanatocin daga Arewacin Najeriya
1. Tartenger Zam - Benue ta Arewa maso Yamma
2. Kaila Samaila Dahuwa - Bauchi ta Arewa
3. Abdul Ningi - Bauchi ta Tsakiya.
4. Khabeeb Mustapha - Jigawa ta Kudu maso Yamma.
5. Rufai Hanga - Kano ta Tsakiya.
6. Abdulaziz Yar’adua - Katsina ta Tsakiya.
7. Mohammed Dandutse Muntari - Katsina ta Kudu.
8. Peter Jiya - Neja ta Kudu.
Jerin mata da ke Majalisar Dattawa a Najeriya
A baya, mun kawo muku labarin cewa akwai wasu mata da suke cikin Majalisar Tarayya bayan gudanar da zabe a shekarar bara.
A zaben 2023, akwai wasu ‘yan siyasa mata da suka lashe zaben Majalisar Dattawa a Najeriya bayan samun nasara tare da doke maza a zaben.
Legit Hausa ta jero muku cikakken sunayen jajirtattun matan guda hudu da ke Majalisar Dattawa ta 10 a Najeriya.
Asali: Legit.ng