Think Tank: Ƴan Arewa Ba Za Su Iya Hana Bola Tinubu Lashe Zaben 2027 Ba Saboda Abu 1

Think Tank: Ƴan Arewa Ba Za Su Iya Hana Bola Tinubu Lashe Zaben 2027 Ba Saboda Abu 1

  • Kungiyar Arewa ta bayyana cewa babu dalilin da zai sa ƴan Arewa su hana Bola Ahmed Tinubu yin tazarce zuwa zango na biyu a 2027
  • Arewa Think Tank ta faɗi haka ne jim kadan bayan kammala taron addu'o'in da ta shiryawa Tinubu na cika shekaru 72 a jihar Kaduna
  • A cewar ƙungiyar, Najeriya ta yi shugaban ƙasa ɗan Arewa na tsawon shekaru 8, don haka ya kamata a sake ba Tinubu dama

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Wata kungiyar Arewa, Think Tank, ta bayyana cewa Arewa ba za ta iya dakatar da kudirin tazarcen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ba a babban zaɓen 2027.

A cewar ƙungiyar, a yanzu Arewa ba ta bukatar karfin siyasa, ta fi buƙatar shugaban da zai kula da shiyyar ta hanyar samar da ababuwan more rayuwa da ilimi.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi abin da zai hana Tinubu yin shekara 8 kan karagar mulki

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Kungiyar Arewa ta shirya wa Tinubu taron addu'o'i a Kaduna Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban Arewa Think Tank, Muhammad Alhaji Yakubu, ne ya bayyana haka yayin da yake amsa tambayoyin ƴan jarida bayan taron addu'o'in ƙarin shekara da suka shirya wa Tinibu a Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma nuna nadama kan yadda ɗan Arewa ya shafe shekaru 8 a kan madafun iko ba tare da ya amfanar da yankin ba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Abin da ya kamata yan Arewa su yi a 2027

Yakubu ya shawarci ‘yan Arewa su fada wa kansu gaskiya duk da tana da ɗaci, su ajiye ra’ayin yanki a gefe, su marawa Tinubu baya a karo na biyu don a samu ci gaba a shiyyar.

A rahoton PM News, ya ce:

"Me zai sa Arewa ta dakatar da Shugaba Tinubu, ta yaya Arewa za ta dakatar da shi a 2027 bayan wani dan Arewa ya yi shekara takwas a kan mulki."

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa 58 sun shiga uku saboda sun kyale an dakatar da Ningi a Majalisa

“Idan muna son mu samu zaman lafiya a kasar nan Arewa ba ta da wani zabi, ba wani zabi da ya wuce a sake zabar Tinubu a karo na biyu domin shi ma ya yi shekaru takwas."
"Abin da ya kamata ƴan Arewa su riƙa tunani a yanzu shi ne yadda za a samu ci gaban ayyukan more rayuwa da bunƙasa harkokin ilimi. Mun yi shugaba ɗan arewa na shekara 8, babu dalilin da zai sa mu hana Tinubu ya yi 8."

Gwamna ya soke naɗin mutane 273

A wani rahoton kuma Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi fatali da naɗe-naɗen hadimai sama da 270 wanda Antoni Janar na jihar Ondo ya yi.

Tun farko dai kwamishinan shari'a, Olukayode Ajulo, ya ce ya naɗa lauyoyi 273 a matsayin masu ba shi shawara domin inganta ayyukan shari'a a Ondo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel