Bashin Kaduna: Shehu Sani Ya Ba Uba Sani Shawarar Matakin da Zai Dauka Kan El-Rufai

Bashin Kaduna: Shehu Sani Ya Ba Uba Sani Shawarar Matakin da Zai Dauka Kan El-Rufai

  • Yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan bashin jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani ya ba Gwamna Uba Sani shawara.
  • Sani ya shawarci gwamnan Kaduna da ya kafa kwamitin binciken tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnan jihar ya yi korafi kan yawan bashi da tsohuwar gwamnatin ta bari a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Sanata Shehu Sani ya ba Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna shawara kan binciken Malam Nasir El-Rufai.

Sani ya ce dole El-Rufai da wadanda ya nada mukamai da 'yan kwangila su amsa tambayoyi kan kudaden da suka salwantar.

Shehu Sani ya dauki zafi kan rikicin Uba Sani da El-Rufai
Shehu Sani ya shawarci Uba Sani ya binciki tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai. Hoto: Nasir El-Rufai, Shehu Sani, Uba Sani.
Asali: Twitter

El-Rufai: Shawarar Shehu Sani ga Uba Sani

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ɗauki zafi kan rikicinsa da ministan Tinubu, ya faɗi dalilin amincewa da sulhu

Sanatan ya ce ya kamata Uba Sani ya kafa kwamitin binciken tsohon gwamnan da mukarrabansa kan tulin bashi a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sannan dole binciken zai hada da bashin $350m da El-Rufai ya ci a lokacin da ya ke gwamnan jihar.

Tsohon sanatan ya bayyana haka ne a shafinsa na X yayin da ya ke martani kan bashin da jihar ke fama da shi.

Sanatan ya koka kan tulin bashin Kaduna

Shehu Sani ya ce ba zai yiwu kawai abin ya wuce da fada a fatar baki ba, ya kamata gwamnan ya cire tsoro ya binciki wadanda ke da hannu a ciki.

"Badakalar da aka yi a Kaduna ba kawai za ta wuce da mita kan bashin ba, ya kamata a cire tsoro a kafa kwamitin binciken tsohon gwamnan da mukarrabansa."

Kara karanta wannan

Jerin sabbin gwamnonin Arewa 7 da suka karbi bashin biliyoyi cikin watanni 6 kacal

"Cikin binciken har da $350m da tsohuwar gwamnatin Kaduna ta karbo bashi, na daɗe da fadan haka zai faru, ga shi yanzu ya tabbata."

- Shehu Sani

An dakatar da shugabar matan APC

A baya, mun kawo labarin cewa jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta dakatar da shugabar matan jamiyyar, Maryam Suleiman.

Maryam da aka fi sani da Mai Rusau ta rasa kujerarta ne bayan caccakar Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna.

Hakan ya biyo bayan zargin cin bashin miliyoyin daloli da gwamnan ya yi kan tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel