Gwamna Ayade Ya Kori Manyan Hadimansa Biyu, Ya Nada Sabbi

Gwamna Ayade Ya Kori Manyan Hadimansa Biyu, Ya Nada Sabbi

  • Gwamnan jihar Kuros Riba, Farfesa Ben Ayade, ya sallami manyan hadimansa guda biyu daga bakin aiki
  • Sakataren watsa labaran gwamna, Christian Ita, ya ce gwamna Ayade ya maye gurbinsu da wasu kuma nan take
  • Ana hasashen dai gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne saboda cin amanar da suka masa ranar zaben Sanatoci

Corss River - Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba, ranar Litinin, ya kori manyan masu ba shi shawara na musamman guda 2 bisa dalilin da ba'a fallasa ba.

Hadiman da gwamnan ya sallama daga aiki sun ƙunshi mashawarci na musamman kan harkokin siyasa a ofishin shugaban ma'aikata, Peter Okaba.

Gwamna Ben Ayade.
Gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade Hoto: Ben Ayade
Asali: Facebook

Baya ga haka, Ayade ya fatattaki mashawarci na musamman kan harkokin sa'ido kan gudanar da ayyukan gwamnati, kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto.

Babban Sakataren watsa labarai na Ofishin gwamna, Mista Christian Ita, ne ya tabbatar da wannan matakin da Ayade ya dauka a wata hira ta wayar salula.

Kara karanta wannan

Abba Gida-gida: Sabon gwamnan Kano ya yi magana, ya fadi abin da ya shiryawa Kanawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Ayade ya maye gurbin mutanen biyu

Bayan sallamar mutanen biyu, Ayade ya umarci Mista Godwin Orim ya maye gurbin ofishin mashawarci na musamman ta fannin sa ido kan gudanar da ayyuka.

Haka zalika ya maye gurbin mai baiwa gwamna shawara kan harkokin siyasa da Romanus Abua, kuma matakin zai fara aiki nan take.

Meyasa gwamnan ya kori hadimansa?

Mista Ita bai bayyana makasudin da ya janyo gwamna ya kori hadiman biyu ba, ya ce dama gwamnan ne ya ɗauke su aiki kuma yana da ikon korarsu idan buƙatar hakan ta taso.

Ya ƙara da cewa Ayade ya umarci tsoffin mashawartan da su guji ayyana kansu a matsayin hadimansa daga yanzu, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Masu sharhi kan yanayin yadda siyasar jihar ke tafiya suna ganin hadiman sun rasa aikinsu ne sakamakon ƙin taimaka wa gwamna a kudirinsa na zama Sanata ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mataimakin Gwamnan Jam'iyyar APC da Ya Sauka Ya Mutu

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC Ta Lallasa PDP, Ta Kwace Mulkin Jihar Benuwai

INEC ta ayyana ɗan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Benuwai da aka gudanar ranar Asabar 18 ga watan Maris, 2023.

Ɗan takarar gwamnan APC kuma babban malamin coci, Rabaran Alia, ya samu nasara kan babban abokin hamayyarsa na PDP mai mulki a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel