Ramadan: Minista Kirista Ya Sake Gwangwaje Musulmai da Kayan Abinci a Arewa

Ramadan: Minista Kirista Ya Sake Gwangwaje Musulmai da Kayan Abinci a Arewa

  • Nyesom Wike, Ministan Abuja shi ma ya ware kayan abinci na makudan kudi domin rabawa al’ummar Musumai a birnin
  • Wike ya raba buhunan shinakafa 5,000 da kwalin suga 1,000 da kuma man gyada domin ragewa al’umma halin kuncin da suke ciki
  • Ministan ya bukaci al’ummar Musulmai da su dage da addu’a domin Shugaba Bola Tinubu ya kara samun lafiya domin inganta kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Ministan Abuja, Nyesom Wike ya gwangwaje al’ummar Musulmai a birnin Abuja da kayan abinci.

Ministan ya yi wannan kyauta ne domin taimakawa Musulmai da suke azumin watan Ramadan a birnin.

Minista Kirista ya raba kayan abinci ga Musulmai a Abuja
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya rabawa Musulmai kayan abinci a birnin. Hoto: Nyesom Wike.
Asali: Facebook

Ire-iren kayan abinci da Wike ya rabawa Musulmai

Kara karanta wannan

Hajj 2024: Gwamnan PDP ya biya rabin kuɗin da aka ƙarawa mahajjatan jihar Arewa, ya faɗi dalili

Daga cikin kayan da Wike ya raba akwai shinkafa buhu 5,000 da taliya katon 1,000 da kuma suga katon 1,000 da sauran kayayyaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan birnin, Samuel Udo Alang ya ce ya ba da kayan ne domin rage wa jama’a radadi.

Ya ce kayan za su tallafa wa al’ummar Musulamai domin buda baki cikin walwala duk da halin kunci da ake ciki, cewar Daily Trust.

Ya kuma bukaci al’ummar Musulmai da su dage da addu’a musamman a wannan lokaci domin samun zaman lafiya.

Wadanda suka ci gajiyar tallafin Wike

Daga cikin wadanda suka ci gajiyar kayan akwai sarakunan gargajiya 17 a Abuja da masallatai da kuma kungiyoyin jin kai, cewar Independent.

Daraktan tsare-tsare a ofishin Ministan, Sani Daura ya ce an yi hakan domin tabbatar da an gudu tare musamman wurin taimakon mazauna birnin a irin wanna lokaci.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya bayyana hanyar da ƴan adawa za su iya tsige shi daga mulki

Babban limamin masallacin gidan Ministan, Ustaz Lawal Mustapha ya godewa Ministan da irin wannan taimako a dai-dai lokacin da ake bukata.

Gwamna Fubara ya biyawa alhazai kudin kujera

A baya, mun ruwaito muku cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya biya cikon kudin kujarun aikin hajji ga maniyyatan jiharsa.

Fubara ya biya dukkan cikon kudin kujerun 41 da ke jiharsa tare da sake siyan karin wasu kujeru shida a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan Hukumar Alhazai ta kara kudin kowace kujera da N1.9m a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel